Siyasa :: Kotun Kolin Najeriya ta wanke Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki kan zargin karya wajen bayyana kadarorinsa. - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Siyasa :: Kotun Kolin Najeriya ta wanke Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki kan zargin karya wajen bayyana kadarorinsa.

<
Kotun Kolin Najeriya ta wanke Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki kan zargin karya wajen bayyana kadarorinsa.
A shekarar 2015 ne gwamnatin Najeriya ta shigar da kara kan tuhume-tuhume 18 na yin karya wajen bayyana abin da ya mallaka.
Tun farko dai Sanata Saraki ya bayyana tuhumar, wacce aka shigar bayan ya zama shugaban majalisar dattawa, da cewa bita-da-kullin siyasa ce kawai.
Duka alkalan kotun kolin biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a Muhammad sun amince da wannan hukuncin, inda suka yi watsi da sauran tuhume-tuhume uku kuma suka ce hujjojin da lauyoyin gwamnati suka gabatar raunana ne.
Masu sharhi na ganin wannan ba karamar nasara ba ce ga Saraki, wanda batun shari'ar ya mamaye mulkinsa na majalisar ta dattawa a shekara ukun da ta gabata.
A watan Yunin bara ne Alkalin kotun da'ar ma'aikata Danladi Umar ya fara yin watsi da tuhume-tuhume 18 da ake wa Saraki.
Daga nan ne sai Ministan shari'ar kasar, Abubakar Malami, ya bayar da umarnin a daukaka kara a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.