Siyasa :: An Fara Kidayar Kuri’u a Zaben Jihar Ekiti - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Siyasa :: An Fara Kidayar Kuri’u a Zaben Jihar Ekiti

<
Rahotanni daga jihar Ekiti na nuni da cewa yanzu haka an fara kidayar kuri’u na zaben gwamnan jihar da ake gudanrwa.
Jama’a sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’unsu a zaben gwamnan jihar da ake gudanarwa a fadin jihar Ekiti.
An dauki matakan tsaro don tabbatar da cewa ba a samu wata matsala ba a zaben, amma duk da haka wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun yi yunkurin tayar da fituna, inda har suka fasa akwatin zabe a wata mazaba.
Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da cafke matasan da suka aikata hakan.
Zaben jihar Ekiti na da muhimmanci kasancewar ita ce kadai jihar da ke karkashin mulkin jam’iyyar adawa ta PDP daga cikin jihohin Yarabawa. Wanda hakan ya sa ita jam’iyya mai mulki APC ke kokarin ganin ta samu nasarar kwace wannan jiha.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.