Siyasa :: Dole a baiwa kabilar Igbo damar shugabancin kasar nan - Sheriff - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Siyasa :: Dole a baiwa kabilar Igbo damar shugabancin kasar nan - Sheriff

<
Tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya bukaci kabilar Igbo dasu goyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya, domin hakan shine zai basu damar samun kujerar shugabancin kasar a shekarar 2023
Dole a baiwa kabilar Igbo damar shugabancin kasar nan - Sheriff
Dole a baiwa kabilar Igbo damar shugabancin kasar nan - Sheriff
Tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya bukaci kabilar Igbo dasu goyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya, domin hakan shine zai basu damar samun kujerar shugabancin kasar a shekarar 2023.
Tsohon gwamnan yayi wannan bayanin ne a lokacin da yake magana da manema labarai a garin Umuahia babban birnin jihar Abia, a lokacin da ya kai ziyara wurin shugabannin jam'iyyar APC na jihar.
"Bisa dukkan alamu da kuma abinda idona yake nuna, jam'iyyar APC ce kadai jam'iyyar da take da karfin da zata iya lashe zaben jihar Abia a shekarar 2019, sannan kuma ina matukar bawa mutanen wannan yanki shawara dasu goyawa shugaba Muhammadu Buhari baya, domin hakan shine zai basu damar samun kujerar shugabancin kasar nan a shekarar 2023.
"Siyasar kasar nan daban ce da sauran kasashe, kabilar Igbo ba zai yiwu ku zauna kawai kuna tunanin cewa za'a dauki kujerar shugabancin kasar nan a danka muku ba; saboda haka indai kun zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari, na tabbata zaku samu kujerar shugabancin kasar nan a shekarar 2023," Inji Sheriff.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.