Siyasa : : Da ni za a buga: Femi Babalola ya shiga cikin sahun masu neman kujerar Shugaban kasa - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Siyasa : : Da ni za a buga: Femi Babalola ya shiga cikin sahun masu neman kujerar Shugaban kasa

<
Ba da dadewa bane mu ka samu labari cewa babban ‘Dan kasuwar nan kuma mai alheri Femi Babalola ya fito neman takarar kujerar Shugaban kasa inda yace shugabancin kasar nan sai da irin su.
Femi Babalola ya bayyana cewa zai yi takara ne a zaben 2019 domin fitar da Najeriya daga kangin da ta samu kan ta. Babalola ya tabbatar da wannan ne ta wani jawabi da ya fitar zuwa ga menema labarai ta hannun Mercy Ayo-Oloye.
Da ni za a buga: Femi Babalola ya shiga cikin sahun masu neman kujerar Shugaban kasa
Femi Babalola zai fito neman takarar kujerar Shugaban kasa a 2019
Mercy Ayo-Oloye wanda ita ce ke jawabi a madadin ‘Dan kasuwar ta bayyana cewa Femi Babalola zai yaki talauci gadan-gadan idan ya hau mulki. Bayan nan kuma Babalola yayi alkawarin yakar masu sace dukiyar Talakawa a kasar.
‘Dan kasuwan dai ya bayyana cewa babban abin da zai maida hankali a kasar idan ya samu mulki shi ne samawa jama’a aikin yi. Babalola yace zai samawa mutum akalla miliyan 10 abin yi cikin shekaru 4 da zai yi a kan karagar mulki.
Bayan nan kuma a jawabin da ta fitar da Mercy Ayo-Oloye ta bayyana cewa Babalola zai tabbatar da cewa ba a dauke wutar lantarki a Najeriya. A zaben 2011 da kuma 2015 Babalola yayi takara a karkashin Jam’iyyar KOWA amma ya sha kashi.
Wannan Attajiri shi ne Shugaban kamfanin nan na mai na Abiye World S. S. L, Oil da kuma Gas-Eur-Afrimpex na Najeriya inda jama’a da dama ke samun na kai wa ciki ta karkashin sa. Babalola yace dole sai irin su sn yi mulki za a ga gyara.
Jiya kun ji cewa wasu Magoya bayan Shugaban kasa Buhari karkashin BSO da ke Kasar nan sun yi gangami a Birnin Tarayya domin nuna goyon bayan su ga Shugaban inda su ke neman ya zarce.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a 

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.