Labaran duniya :: Za a yi yakin da ba a taba irinsa ba idan Amurka ta taba Iran - Rouhani - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran duniya :: Za a yi yakin da ba a taba irinsa ba idan Amurka ta taba Iran - Rouhani

<
Shugaban Amurka Donald Trump da kuma shugaban Iran, Hassan Rouhani, sun yi musayar yawu suna yi wa juna gargadi mai zafi, a lokacin da danganta tsakanin kasashen biyu ke kara tabarbarewa.
Mista Trump ya wallafa sakon Twitter mai cewa Iran za ta "sha irin wuyar da kasashe kadan ne suka taba sha a tarihi" idan ta yi wa Amurka barazana.
Daga farko dai Mista Rouhani ya ce yaki da Iran zai kasance "yakin da ba taba ganin irinsa ba a duniua".
A watan Mayu ne Amurka ta fice daga wata yarjejeniyar da ta rage shirin nukiliyar Iran domin a janye takunkuman da aka kakaba mata.
Amsoshin tambayoyinku kan rikicin Iran da Isra'ila
Trump ya janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran
A yanzu haka Amurka tana sake kakaba takunkuman, duk da cewar Birtaniya da Faransa da China da Rasha da kuma Jamus, wadanda suka rattaba hannu a yarjejeniyar ta shekarar 2015, sun ki amincewa da matakin Amurkar.
Kalaman Shugaba Rouhani, wadanda ya yi wa jami'an diflomasiyyar Iran, sun nuna yiwuwar ci gaba da huldar kasar da Amurka nan gaba.
"Ya kamata Amurka ta san cewar zaman lafiya da Iran shi ne zaman lafiyar da ya fi kowanne, kuma yaki da Iran zai zamo yakin da ba a taba yin irinsa ba," kamar yadda kamfanin dillancin labaran Iran, Irna, ya ambato shugaban Iran din yana cewa.
Kalaman bacin ran Mista Trump na kama da irin yadda ya yi maganganu kan shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un, a shafinsa na Twitter , mutumin da ya cewa "mahaukaci" wanda "za a yi wa irin jijjigar da ba a taba yi ba."
Duk da haka musayar kalaman nasu ne ya rikida ya zama tattaunawar diflomasiyyar da ake yi a yanzu.
A ranar Litinin, wani babban kwamanda na rundunar dakarun kiyaye juyin-juya halin Musulunci ya nuna cewar kalaman shugaban Amurka din suna daga cikin wasu dabaru.
Kamfanin dillancin labaran daliban Iran ya ambato Gholamhossein Gheybparvar yana cewa: "Kalaman Trump din a kan Iran kalamai ne na yakin baka kuma zai sha mamaki idan ya yi kokarin daukar mataki a kan Iran".
'Kama da mafiya(kungiyar masu aikata miyagun laifuka)'
Ranar Lahadi, Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce yana son ya hana wasu kasashe sayen man Iran zuwa karshen watan Nuwamba a matsayin wani mataki na kara matsin lamba a kan Tehran.
A lokacin da yake gabatar da jawabi ga wasu Amurkawa 'yan asalin kasar Iran a California, Mista Pompeo ya ce gwamnatin ta Iran "ta fi kama da ta 'yan mafiya, (kungiyar masu aikata miyagun laifuka) fiye da gwamnati".
Mista Pompeo ya bayyana Mista Rouhani da kuma ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif, wanda ya jagoranci yarjejeniyar nukiliyar "a matsayin wasu wakilai wajen damfarar kasashen waje ta jagororin addinin musulunci na kasar (Ayatollah)".
Wannan taron ne karon farko da wani babban jami'in Amurka ya gabatar da jawabi ga 'yan Amurka 'yan Asalin Iran da suka kai haka yawa, in ji wakiliyar BBC kan ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Barbara Plett Usher.
Ana ganin wannan daya ne daga cikin matakan kara matsin lamba ga shugabannin Iran.
Akan mene ne Amurka da Iran ba su amince da juna ba?
Mista Trump ya dade yana nuna rashin yarda da yarjejeniyar nukiliyar 2015, wadda ta sa Amurka sallamar da kadarori na biliyoyin daloli da ta rike domin Iran ta rage shirin nukiliyarta
Gwamnatin Shugaba Trump tana ganin Iran ce ke janyo tashin hankali a Gabas Ta Tsakiya, yana mai cewa yarjejeniyar nukiliyar ta bai wa Iran damar gindaya manufar iko a yankin.
Iran ta tura daruruwan dakaru da kuma dubban mayakan sa-kai zuwa Syria, kuma ta karfafa karfin sojinta a wurin
Kasashen tekun Fasha sun zargi Iran da mara wa 'yan tawayen Houthi na Yemen baya da kudi da kuma makamai, sai dai Iran ta musanta hakan.
Saudiyya, wata muhimmiyar kawar Amurka, wata babbar abokiyar hammayar ce ga Iran kuma ta dade tana gargadi game da manufofin Iran
Daga farko dai Washington ta yi kokarin tilasta wa dukkan kawayenta su daina sayen man Iran, sai dai kuma a yanzu ta ce za ta iya ba da dama ga wadanda suka dogara akan man Iran
An yi ikirarin cewar Shugaba Rouhani, ya yi barazanar yamutsa jigilar mai daga kasashe masu makwabtaka idan aka hana sayen man Iran din.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.