Siyasa::Da dumin sa: Shugaba Buhari ya soke zaman majalisar zartarwa na wannan mako - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Siyasa::Da dumin sa: Shugaba Buhari ya soke zaman majalisar zartarwa na wannan mako

<
Ba za a yi zaman majalisar zartarwa, da aka saba yi duk sati ba, wannan makon, kamar yadda jaridar Daily Post ta rawaito.
Jaridar ta bayyyana cewar, shugaba Buhari ya soke zaman na wannan makon ne saboda zai saka hannu a kan kasafin kudin shekarar 2018 da majalisa ta amince da shi. Ana saka ran shugaba Buhari zai saka hannu a kan kasafin kudin a ranar ta Laraba.
Da dumin sa: Shugaba Buhari ya soke zaman majalisar zartarwa na wannan mako
Shugaba Buhari yayin zaman majalisar zartarwa
Shugabannin majalisun tarayya; Bukola Saraki da Yakubu Dogara, na daga cikin mutanen da fadar shugaban kasa ta gayyata domin halartar sahidar saka hannu a kan kasafin kudin da za a yi a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.
Tun a satin da ya gabata ne mai Magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina, ya kyarawa ‘yan Najeriya cewar a wannan satin da muke ciki shugabab Buhari zai saka hannu a kan kasafin kudin.
A ranar 16 ga watan Mayu ne majalisar tarayya ta zartar da kasafin kudin shekarar 2018 bayan gabatar da shi gaban su a watan Disamba na shekarar 2017.
‘Yan Najeriya sun zargi majalisa da jan kafa wajen zartar da kasafin kudin duk da kasancewar shugaba Buhari ya gabatar das hi gaban su a kan lokaci.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.