Siyasa :: Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin kasar na 2018 a fadarsa da ke Abuja. - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Siyasa :: Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin kasar na 2018 a fadarsa da ke Abuja.

<
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin kasar na 2018 a fadarsa da ke Abuja.
A tsakiyar watan Mayu ne majalisun dokokin kasar suka amince da kasafin kudin, wanda ya kai naira tiriliyon 9.1, wata shida bayan da shugaban ya gabatar musu da shi.
Hakazalika 'yan majalisun sun kara adadin kasafin daga naira miliyan 500 zuwa tiriliyon 8.6.
'Yan majalisar sun kuma kara adadin farashin man fetur da gwamnati ta tsara kasafin a kai daga dala 45 zuwa 51, suna masu cewa hakan ya zama dole saboda ganin yadda farashin man ya tashi a kusuwannin duniya.
Wani masanin tattalin arziki Farfesa Nazifi Darma, ya shaida wa BBC cewa rashin sanya hannu kan kasafin kudin a kan lokaci yana yin tasiri ga ci gaban habakar tattalin arzikin kasar.
"Gwamnati na da tasiri matuka kan tattalin arzikin Najeriya, a don haka jinkirin da ake samu babu shakka zai shafi tattalin arzikin kasar," a cewar Farfesa Darma, wanda malami ne a jami'ar Abuja.
Zamanin Buhariyya: Wa ya karya tattalin arzikin Najeriya?
Da gaske Nigeria ta fita daga matsin tattalin arziki?
Sai dai malamin ya yaba da yadda aka ware kudade ga fannin noma, yana mai cewa hakan zai taimaka wuirn samar da ayyukan yi.
Tattalin arzikin Najeriya na farfadowa a hankali bayan da ya fuskanci mummunan koma-baya a shekarar 2016.
Shugaba Muhamnmadu Buhari, wanda aka zaba a 2015, bisa alkawarin yaki da cin hanci da samar da ayyukan yi, na neman wa'adi na biyu a zaben badi.
Sai dai wasu na sukar yadda ya fuskanci matsalar tattalin arzikin, duk da cewa yana bugar kirjin samun nasarori.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.