Labaran siyasa :: Shugaba Buhari ya nemi afuwa kan Abiola - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa :: Shugaba Buhari ya nemi afuwa kan Abiola

<
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi afuwar iyalan marigayi Moshood Abiola a madadin gwamnatin kasar bisa soke sakamakon zaben shugaban kasa na watan Yunin 1993.
An dai kyautata zaton cewa Mr Abiola ne ya lashe zaben, wanda gwamnatin Ibrahim Babangida ta soke, tun kafin a kai ga bayyana sakamakonsa.
Ya ce: "A madadin gwamnatin tarayya, ina nema wa kasar nan afuwa daga iyalan marigayi MKO Abiola wanda ya samu kuri'u mafiya yawa da kuma wadanda suka rasa 'yan uwansu a fafutukar 12 ga watan Yuni".
Ya kara da cewa ba an shirya taron ba ne domin fama ciwon da lamarin ya haifar ba, sai dai kawai domin kawar da mummmunan tasiri, da bakin cikin da ke tattare da abin da ya faru.
A don haka ya yi kira ga 'yan kasar da su karbi abin da ya faru na soke zaben da zuciya daya.
Hotunan yadda Buhari ya karrama Moshood Abiola
Abiola mai tsoron Allah ne — Zainab Abiola
Wakilin BBC Ishaq Khalid ya ce wurin ya kaure da tafi a lokacin da shugaban ya bayyana neman afuwar.
Ya kara da cewa wasu da dama daga cikin mahalarta taron sun kadu da kalaman nasa.
Shugaba Buhari ya mika wa dan marigayin Kola Abiola lambar GCFR a madadin mahaifinsa.
Har ila yau an girmama Babagana Kingibe wanda ya tsaya a matsayin mataimakin Abiola.
Hakazalika an bai wa marigayi Gani Fawehinmi wato wani babban lauya wanda ya yi ta fadi tashi game da ranar tunawa da zaben 12 ga watan Yunin.
Taron ya samu halartar manyan jami'an gwamnati da kuma masu fafutukar ganin an girmama wannan rana ciki har da fitaccen marubucin nan Wole Soyinka.
Sai dai babu wani daga cikin tsaffin shugabannin kasar da ya halarta.
Janar Ibrahim Babangida ya aika sakon uzurin rashin lafiya yayin da Olusegun Obasanjo ya ce yana wajen kasar domin halartar wani taro.
Hakazalika shugabannin majalisun dokokin kasar ba su halacci taron ba.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.