Labaran duniya :: A wacce kasa fetur ya fi araha da kuma tsada a duniya? - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran duniya :: A wacce kasa fetur ya fi araha da kuma tsada a duniya?

<
Tsayawa domin sayen man fetur ba sabon abu ba ne ga mutane. Ko da yake wannan ya danganta ne da kasar da mutum ya ke zaune, a kan haka akwai bambanci game da yawan kudin da za a kashe.
Duk da cewa ana samun fetur da man disel a ko wanne sako-sako na duniya, kuma dukkanin kasashen duniya na sayen man fetur a kasuwanin duniya, amma ko wacce kasa na da farashinta.
Haraji da tallafin da gwamnatin ta ke bayarwa da farashi mai da hauhawar farashin kayayyaki duk suna cikin abubuwan da ke shafar farashin mai.
Idan kasa ce da ke fitar da mai ko kuma shigo da mai shi ma farashin fetur zai bambanta.
A bayanne take cewa kudin da mutum zai biya zai ninka sau 200 a kan lita daya ta mai, ko da yake wannan ya danganta ne a wurin da ka yi siyayya.
Farashin fetur mai rahusa
Venezuela: Ita ce kasar da ake sayar da man fetur da arha a duniya a cewar wani rahoto na cibiyar kayyade farashin mai ta duniya, watau Global Petrol Prices, da aka wallafa a ranar 28 ga watan Mayu 2018.
Cibiyar, wadda ta ke nazari kan alkaluman da ake fitarwa daga kasashe 167 da kuma yankuna ta ce ana sayar da lita daya ta fetur a Venezuela kan dala 0.01, duk da cewa tattalin arzikinta na fuskantar koma baya kuma tana fama da hauhauwar farashin kayayyaki.
Dalilin da yasa mai ba shi da tsada a kasar?
Venezuela ita ce kasar da ta fi yawan arzikin mai a kasa duk da cewa tana fuskantar koma baya a tattalin arzikinta, amma har yanzu gwamnati na bayar da tallafi kan akasarin albarkatun man fetur din kasar.
A dayan bangaren kuma akwai kasar Saudiyya wadda ita ce kasa ta biyu mai arzikin mai, amma ita ce ta 14 wajen sayar da fetur da arha a duniya, inda ake sayar da lita daya ta man fetur a kan dala $0.54.
Fetur na da arha a Iran inda ake sayar da lita daya ta man fetur da arha kan dala $0.28 da kuma Sudan in da ake sayar da lita guda a kan $0.34, kuma dukanninsu kasashe ne masu arzikin man fetur.
A kasar Kuwait dala $0.35 ake sayar da lita guda ta mai, yayin da a Algeriya dala $0.36 ake sayar da lita daya na man fetur.
Gwamnatocin wadannan kasashe sun amince a rika sayar wa al'umominsu man fetur a farashi mai rahusa, sai dai wannan ya sa ba sa samun riba sosai.
Sai dai man fetur da suke fitar wa zuwa kasashen waje da suke sayar wa a kasuwannin duniya zai sa su samu gagarumar riba.
Farashin man fetur ya tashi a cikin watanni 12 da suka gabata - kuma idan lamura suka ci gaba a haka (kamar yadda masana suka yi hasashe), to zai yi wuya wadannan gwamnatoci su cigaba da sayar da man fetur a farashi mai arha ga al'ummominsu.
Kasashen da ake sayar da man fetur da tsada
Iceland: Ita ce kasar da ta fi sayar da man fetur da tsada a duniya inda ake sayar da lita guda ta man kan dala 2.17, a cewar kungiyar kayyade farashin man fetur ta duniya.
Yankin Hong Kong na China shi ne na biyu inda ake sayar da lita guda ta man fetur a kan dala 2.14 - watau ta fi ta Venezuela tsada sau 194.
Sai dai kasar da ta ba da mamaki ita ce Norway, wadda ita ce kasa ta uku da ke sayar da man fetur da tsada inda mutane ke sayen lita guda a kan dala 2.05, duk da cewa tana cikin masu arzikin man fetur.
Gwamnatin Norway ta sanya haraji kan man fetur domin ta rage yawan amfani da motoci daga wurin mutane, kuma domin ta karfafa mu su gwiwar amfani da sufurin gwamnati.
Ribar da kasar ta ke samu daga man da ta fitar zuwa kasashen waje tana adana su ne a cikin asusun kauce wa bacin rana, watau Sovereign Wealth Fund, da ake kira Oljefondet , kuma an yi kiyasin cewa shi ne asusu ma fi girma a duniya.
Manufar asusun ita ce tattalin arzikin kasar ba zai dogara a kan man fetur kadai ba, kuma kasar ba za ta shiga cikin matsala ba ko da man fetur dinta ya kare.
Netherlands na sayar da lita guda ta mai a kan dala 1.97. Sai kuma Monaco da Girka da kuma Denmarkinda ake sayar da lita guda a kan dala 1.92
Sai dai matsalar durkushewar tattalin arziki ce ta sa Girka ta kara farshin mai kamar yadda kasashen duniya masu ba da bashi suka bukace ta karkashin ka'idojin ceto tattalin arzikin kasar da suka cimma.
Israila: Ita ma wata kasa ce da ke sayar da man fetur da tsada sakamakon yawan harajin da ake biya.
Ana sayar da lita guda ta mai kan dala 1.88 kuma ita ce ta tara a cikin jerin kasashen duniya masu sayar da mai da tsada a cewar cibiyar kayyade farashin man fetur ta duniya.
Is'raila na sayar da man fetur da tsada ne saboda tana shigo da galibin man da ta ke amfani da shi daga ketare, kuma kasashen da ba kawayenta ba ne ke sayar mata da man a cewar majiyoyin gwamanati.
Yadda ake tsara farashin man fetur
Kamfanin mai na Brazil watau Petrobras ya ce idan ya zo kan batun farashi mai, to wannan ya ta'alaka ne a kan wasu abubuwa uku kan farashin da kasashen da suke fitar da mai da kuma wadanda a kai wa man suka kayadde, da yawan harajin da ko wace gwamnati ta amince ta sa, da kuma ribar da mutum ko kamfanin da ya sayar da man zai samu.
Ko wanne bangare na da rawar da ya ke takawa, haraji da kuma tallafin da ko wacce kasa ta ke bayar wa za su sa a samu bambanci a farasahin man fetur a kasashe daban-daban.
Karfin sayan man fetur
Wannan wani abu ne da ya kamata a duba, wato karfin sayen man fetur tsakanin al'umma.
Alal misali watakila an sayar da mai da tsada a Netherlands fiye da Bolivia, sai dai wannan ba wai yana nufin cewa man ya fi karfin 'yan kasar Netherlands ko kuma' yan Bolivia suna da karfin sayen man fetur din.
Wannan ya danganta ne a kan kudin da ka ke da shi a hannunka.
Labarai masu alaka

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.