Labaran duniya :: Shugabar kasar New Zealand Jacinda Ardern ta haifi 'ya mace - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran duniya :: Shugabar kasar New Zealand Jacinda Ardern ta haifi 'ya mace

<
Firai ministar New Zealand Jacinda Ardern ta haifi 'ya mace ta farko mai nauyin kilogram 3.31.
Hakan ya sa ta kasance shugabar kasa ta biyu a zamanin nan da ta haihu a lokacin da take kan karagar mulki.
An kai Misis Ardern wani asibiti da ke garin Auckland da safiyar ranar Alhamis, kwana hudu kafin lokacin haihuwarta.
Firai ministar mai shekara 37 ta dauki hutun makoni shidda domin kula da jaririyarta kuma ta mika ragamar mulki ga mataimakin firai ministan kasar Winston Peters.
Sai dai ta ce za ta ci gaba da sa ido a kan yadda za a tafiyar da harkokin gwamnati.
Da misalin karfe 04:45 na agogon GMT shugabar kasar ta haihu.
Daga bisani Misis Ardern ta sanar da labarin haihuwarta a shafukan sada zumanta tana mai cewa tana ji kamar ta tsinci dami a dala kuma ta yi wa ma'aikatan asibitin godiya.
A cikin sanarwar da ta fitar ta ce : "Tabbas na san muna jin yadda sabbin iyaye suke ji a lokacin da suka samu karuwa amma kuma ina son na nuna godiya ga mutanen da suka kula da ni da kuma wadanda suka yi mata fatan alheri. Na gode ."
An tsawaita wa mata hutun haihuwa a Najeriya
An samu raguwar haihuwa a Amurka
'Yan siyasa sun rika tura mata sakonnin taya murna, ciki har da sakon da tsohuwar firai ministar New Zealand Helen Clark ta tura mata a shafin Twitter da kuma firai ministan Ostriliya Malcolm Turnbull.
A watan Oktoban da ya gabata ne aka zabi Misis Ardern, kuma a watan Janairun da ya gabata ne ta yi shellar cewa ita da saurayinta Clarke Gayford za su samu karuwa nan ba da jimawa ba.
"Ba ni ce mace ta farko da take abubuwa na komai da ruwanka ba".
"Ba ni ce mace ta farko da ke aiki kuma ta haihu ba; akwai mata da dama da suka yi haka a baya," Ta bayyanna hakan ne a wata hira da ta yi da wani gidan rediyon New Zealand a farkon bana.
Mai jegon ita ce firai minista mafi kankantar shekaru da aka samu a kasar tun bayan shekarar 1856.
A shekarar 1990, Benazir Bhutto ta haifi 'ya mace tana rike da mukamin firai ministar Pakistan, kuma ita ce haihuwar farko da wata zababbiyar shugabar kasa za ta yi a lokacin.
Madam Ardern ta kuma haifi jaririyarta ne a ranar da aka haifi marigayiya Benazir Bhutto.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.