Labaran duniya :: An hana 'yan Najeriya shiga filin wasa da kaji - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran duniya :: An hana 'yan Najeriya shiga filin wasa da kaji

<
An hana 'yan Najeriya magoya bayan kungiyar Super Eagles zuwa da kaji cikin filayen wasan kwallon kafa a Rasha.
An ruwaito ministan al'adu da yawo bude ido na Rasha Andrei Ermak na cewa:
"Cibiyar watsa labarai da muka samar na samun tambayoyi da dama: inda wasu 'yan Najeriya masu goyon bayan kungiyar Super Eagles suka nemi izinin shiga cikin filayen wasanni da kaji masu rai, domin wanna alama ce tasu, kuma su kan je da kaji wajen dukkan wasanninsu. Amma mun sanar da su cewa shiga wurin da kaza mai rai ba abu ne mai yiwuwa ba."
Amma ya ce ba za a hana 'yan Najeriya masu kallon wasannin a wajen filayen wasan su tafi can da kajin nasu ba:
"Babu damuwa, za mu iya sanar da su ma inda ake sayar da kaji idan suna bukatar su."

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.