Siyasa : Kwankwaso ba zai iya hana Buhari cin kano ba - El-Rufa'i - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Siyasa : Kwankwaso ba zai iya hana Buhari cin kano ba - El-Rufa'i

<
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce barazanar ficewar da wasu jigan-jigan jam'iyyar APC ke yi daga jam'iyyar ba zai hana Shugaba Muhammadu Buhari yin nasara ba a zaben 2019.
A kwanakin baya ne wasu manyan 'yan siyasa da suka canza sheka daga PDP zuwa APC a 2014 suka yi zargin cewa ba a damawa da su tare da barazanar daukar mataki idan har ba a biya bukatunsu ba.
Manyan 'yan siyasar sun hada da tsoffin gwamnonin Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da na Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamakko, da na Rivers, Rotimi Amaechi, da na Gombe, Danjuma Goje, da na Kwara Bukola Saraki.
Sai dai Gwamna el-Rufa'i ya ce, "'yan siyasar ba su da wani tasiri, kuma Shugaba Buhari zai lashe dukkan jihohinsu a zaben 2019."
Wasu na ganin wannan wani sabon rikici ne ya kunno kai a jam'iyyar APC, baya ga rikice-rikicen da ta ke fama da su na cikin gida a jihohi.
Kuma suna ganin zai iya yi wa jam'iyyar illa a zabukan na badi.
Wasu jiga-jigan APC sun gargadi Buhari da kuma jam'iyyar
Buhari bai iya mulki ba — Shekarau
Saraki ko Kwankwaso: Wa zai iya ja da Buhari a APC?
Da yake magana da manema labarai ranar Talata bayan ganawa da Shugaba Buhari a Abuja, Gwamna Nasir el-Rufai, ya ce "tun shekarar 2003 shugaban ke lashe zabe a Kano."
Gwamnan ya kara da cewa, ko da sun yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar APC, hakan ba zai hana shugaba Buhari tasiri a jihohin tsoffin gwamnonin ba.
"Shugaba Buhari zai yi nasara a jihohin Sakkwato da Kwara da Adamawa cikin sauki, kuma ya riga ya gama samun nasara a jihar kano," a cewar el-Rufa'i.
Gwamnan na Kaduna kuma ya ce idan aka dubi yadda dubban mutanen da suka fito domin yi wa Shugaba Buhari maraba, za a ga cewa Kano wuri ne da shugaban ya ke da magoya baya sosai.
Ya kuma ce, hakan ya faru ne ba tare da tawagar Tsohon Gwamna Rabi'u Kwankwaso ba.
Sai dai gwanan ya ce akwai bukatar duba koke-koken da jiga-jigan jam'iyyar ta APC suka rubutawa uwar jam'iyyar da idon basira saboda siyasa, "harka ce da ke bukatar karuwar jama'a ba raguwa ba."
Amma ya ce bai kamata manyan 'yan siyasar su yi barazanar ficewa daga jam'iyyar ba.
A baya-baya nan ne tsoffin gwamnonin wadanda suka koma jam'iyyar daga PDP suka soki yadda APC ta ke tafiyar da harkokinta da kuma gwamnatin Shugaba Buhari.
'Yan siyasar sun yi zargin cewa ba a "damawa da su a harkokin jam'iyyar da kuma gwamnati, sannan ana nuna mu su wariya da kokarin dakile su ta kowacce hanya."
Sun ce "Rotimi Amaechi da kuma Jummai Alhasan ne kawai aka bai wa manyan mukaman siyasa a cikin gwamnatin Shugaba Buhari."
Wadannan kalaman na kunshe ne a wata wasika ta suka aika wa shugaban jam'iyyar da kuma Shugaba Buhari, wadda Alhaji Kawu Baraje da Olagunsoye Oyinlola (wanda tuni ya fice daga jam'iyyar ta APC zuwa ADC) suka sa wa hannu a ranar 17 ga Afrilu, inda suka ce ya kamata a ji kukansu idan har ana son yin nasara a zaben 2019.
A ranar Talata ne wa'adin da suka ba jam'iyyar APC ya kawo karshew, sai dai kawo yanzu ba su bayyana mataki na gaba da za su dauka ba.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.