Siyasa : Ana ce-ce-ku-ce kan hoton Buhari a wurin tafsiri - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Siyasa : Ana ce-ce-ku-ce kan hoton Buhari a wurin tafsiri

<
'Yan Najeriya suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da wani hoton Shugaban Kasar Muhammadu Buhari da aka wallafa lokacin da ya halarci tafsirin Al-Kur'ani a fadarsa da ke Abuja.
A ranar Alhamis, wato ranar farko ta fara azumin watan Ramadan, fadar shugaban ta yada hoton a shafukan sada zumunta.
BBC ta samu dimbin ra'ayoyin jama'a a shafukanmu na sada zumunta bayan wallafa hoton musamman a shafinmu na Facebook .
Wasu 'yan kasar sun bayyana halartar tafsirin da cewa siyasa ce kawai, ganin cewa zabe ya karato kuma shugaban na neman wa'adi na biyu.
Yayin da magoya bayan shugaban suke kare halartar tasa, suna masu yaba masa da kuma yi masa addu'ar samun nasara da karin lafiya.
Adams Babangida cewa ya yi:
"Ko me yake saurare oho... A gaya masa gidajen talakawa da yawa yanzu haka an sha ruwa ba su da abin kai wa baki, sakamakon irin tashin gauran zabi da abubuwan masarufi suka yi kawai don an cire talafin da a baya yake talafa wa talakawan."
Hakazalika shi ma Frankling Auwal nuna damuwarsa ya yi game da halin da talakawan kasar suke ciki:
"Ina ruwan talaka da jin tafsirin shi, ya sauke nauyin mutane da ke kan shi, talaka bai zabe shi ba don a nuno shi ya je tafsir ba."
Hotunan yadda Musulmin duniya suka sha ruwa
Mata-maza za su iya aure har da haihuwa - Sheikh Daurawa
Amma Hassan Muhammad shi nuna farin cikinsa ya yi dangane da batun:
"Alhamdulillah wannan irin abin farin ciki da ba zai misaltuba. Ga shugaban kasata yana sauraron tafsir. Allah Ya kara maka lafiya. Allah Ya baka ikon ci gaba da ayyukan alheri. Mun gode da ganinka a cikin wannan yanayi mai ban sha'awa."
Wani dan jarida a kasar Abdulaziz Abdulaziz shi ma ya bayyana ra'ayinsa dangane da batun kamar haka:
Jama’a a taya ni dubawa. Wai su malaman Villa ko tafsirin nan ba kakkautawa suke yi ne, bana azumi ba kawai? Na ga daga...
Posted by Abdulaziz Abdulaziz on Thursday, 17 May 2018
Shi ma wani dan jarida a kasar Jafar Jafar ya bayyana ra'ayinsa:
Posted by Jaafar Jaafar on Friday, 18 May 2018
Ga sauran wadansu ra'ayoyin jama'a - ku ma za ku iya bayyana ra'ayoyinku a shafin namu na Facebook :
Karanta karin wasu labaran
Buhari ya yi tsokaci kan maganar da ya yi kan matasa
Wurare hudu da Buhari da Trump ke kamanceceniya da juna?

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.