Islamic : Me ya kamata a kauracewa a shafukan sada zumunta lokacin Ramadan? - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Islamic : Me ya kamata a kauracewa a shafukan sada zumunta lokacin Ramadan?

<
Shafukan sada zumunta da muhawara na zamani wasu hanyoyi ne da al'umma ke amfani da su domin cimma bukatu daban-daban: wasu na neman ilimi, wasu kasuwanci, wasu kuwa na yin amfani da su ne domin watsa labaran karya da kuma cin zarafin jama'a.
Mutanen da suka samar da wadannan shafuka irinsu Facebook da Twitter da WhatsApp da Instagram da makamantan su sun sanya sharuddan amfani da su, cikinsu har da hana cin zarafin wani ko wasu, hana sanya hotunan batsa ko yin kalaman batanci da na batsa da dai sauransu.
Da ma dai tsarin zamantakewar Musulmi, wanda akasari addini ke jan linzaminsa, ya sanya sharuddan zaman tare.
Addinin Musulunci yana gaba-gaba wajen tabbatar da 'yancin dan adam da kuma tsawatarwa kan abubuwan da ba su dace ba, don haka ne malamai ke kara yin kira ga masu amfani da shafukan sada zumunta su kiyaye dokokin addinin a lokacin da suke yin amfani da shafukan.
Mun tattauna da Malam Musa Sani, limamin daya daga cikin masallatan rukunin gidaje na Efab da ke Abuja, babban birnin Najeriya, kuma ya yi mana karin bayani:
Ƙarya
Ƙarya na cikin manyan abubuwan da addinin Musulunci ke ƙyamar su. Ayoyi da dama a cikin Al-Ƙur'ani mai tsarki sun yi gargaɗi a kan karya, inda suke bayyana irin azabar da Allah ya tanadar wa maƙaryata.
Kazalika, hadisai da dama sun bayyana makaryata a matsayin mutanen da ba a bukatar azuminsu.
Misali, wani hadisi da Abu Huraira ya rawaito ya ambato Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "Duk mutumin da bai daina karya ba, Allah ba ya bukatar sa da ya daina cin abinci ko shan abin sha (wato Allah ba zai karbi azuminsa ba.)".
Haka kuma wani hadisin na cewa, "Na hore ku da ku guji yin karya, domin mai yin karya za a rubuta sunansa a matsayin makaryaci."
Da alama masu amfani da shafukan sada zumunta na zamani da dama ba sa yin la'akari da irin wannan hadisi a lokutan azumi, ganin yadda suke watsa labarai na karya.
Yada jita-jita
Masu amfani da shafukan sada zumunta da muhawara sun yi fice wajen yada jita-jita, lamarin da sau da dama kan haifar da mummunan sakamako.
Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce, "Ya ishi mutum zunubi a ce duk labarin da ya ji sai ya yada shi."
Hakan na nuna cewa ya kamata mutanen da ke amfani da wadannan shafuka su rika yin kaffa-kaffa wajen irin kalaman da suke watsawa.
Batsa
Hotuna da bidiyo da kuma kalaman batsa na daga cikin abubuwan da suka mamaye shafukan sada zumunta da muhawara.
Haka kawai, babu kunya, za ka ga masu amfani da shafukan suna sanya batsa, kuma suna yin tsokaci a kansu.
Yawancin lokuta ma sukan tura su ga abokansu da ke shafukan, ko da kuwa ba su nemi a tura musu ba. Hakan yakan fusata mutane da dama.
Addinin Musulunci yana matukar kyamar wannan mummunar dabi'a, wacce Allah da Annabinsa Muhammadu (SAW) suka haramta
Jin kade- kade
Jin kade-kade da wake-wake na cikin abubuwan da aka yi hani da su a Addinin Musulunci idan ba a wasu lokutan kebabbu ba, musamman inda aka amince mata su yi kida da waka a lokutan biki.
Ko su ma ba a yarda su bayyana al'aurarsu a lokacin da suke waka ba.
Don haka masu amfani da shafukan zumunta na zamani su guji fadawa irin wannan tarko, ganin yadda shafin intanet ya cika makil da kade-kade da wake-wake wadanda wasunsu ma na batsa ne.
A takaice dai, za a iya cewa dukkan abubuwan da Musulunci ya yi hani da su a lokutan da ba a azumi, su ne kuma wadanda ya yi hani da su a lokacin azumi.
Kuma babban abin da za a yi la'akari da shi shi ne fadin Manzon Allah Muhammad (SAW) cewa, "Ku fadi alheri ko ku yi shiru". Don haka ya kamata masu amfani da shafukan zumunta su tambayi kansu: shin abubuwan da zan wallafa, ko na kalla, ko kuma na fada, suna da gurbi a Addinin Musulunci?
Kazalika, idan wani ya zungure su domin neman fada ko maganar da ba ta dace ba, ya kamata su ce masa "Mu muna azumi", kamar yadda Manzon Allah ( SAW) ya bukaci a yi.
An sabunta wannan makala ce daga wacce aka rubuta ranar

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.