Labaran wasani : Mohamed Salah: Kun san Balaraben da ya 'gagari' Turawa? - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran wasani : Mohamed Salah: Kun san Balaraben da ya 'gagari' Turawa?

<
Kwanaki biyu bayan Mohamed Salah ya karbi kyautar gwarzon dan wasan Ingila na bana, dan wasan na Masar ya sake nuna kansa a Turai, a matsayin wanda zai iya zama gwarzon dan wasan duniya.
Salah ya kayatar da magoya bayan Liverpool da duk wani masoyin kwallon kafa a duniya a yayin da Liverpool ta lallasa Roma da ci 5-2 a gasar zakarun Turai a karawar farko na zagayen daf da na karshe.
Kwallo biyu Salah ya ci sannan ya bayar aka ci biyu a daren da magoya bayan Liverpool ba za su taba mantawa ba a Anfield.
Yanzu kwallo 43 Salah ya ci a wasa 47 a kakar bana, kwazon da ya sa wasu ke kwatanta dan wasan da fitattun 'yan kwallo irinsu Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da kuma Neymar.
Wannan ya sa wasu ke ganin Salah ya cancanci ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya ta Ballon d'Or.
Abin mamaki shi ne yadda wannan Balarabe, dan kasar Masar, ya zo ya daga tuta a cikin Turawa, acewar wasu masu sharhi kan al'amuran wasanni.
Babu wani Balarabe da ya taba yin irin bajintar da Mo Salah yake yi.
Yadda Mo Salah ya yi kaca-kaca da AS Roma
'Yan Liverpool na 'kaunar Musulunci' saboda Salah
Tsohon dan wasan Wales Robbie Savage ya shaida wa BBC cewa: "Dole ne a ba shi Ballon d'Or," bayan kwallo biyun da Salah ya jefa a ragar Roma.
Ya ce Salah yana da kyau, "Kada a damu da kyautar PFA da ya lashe, kawai a ba shi Ballon d'Or."
Tsohon dan wasan Liverpool Robbie Fowler wanda aka taba zaba domin lashe kyautar a 1996, ya bayyana Salah a matsayin "dan wasa mai ban mamaki".
Kishirwar wasan karshe a Kiev zai tabbata idan har Liverpool ta kammala aikinta a Rome a karawa ta biyu.
Idan an kammala gasar zakarun Turai ne kuma, Salah zai sake nuna kansa a duniya, a yayin da zai jagoranci Masar a gasar cin kofin duniya a Rasha.
Salah ne dan wasan Afirka na farko da ya ci kwallo akalla tara a kakar wasa a tarihin gasar zakarun Turai.
Salah ya jefa kwallo a raga a wasa biyar a jere da aka fara da shi a gasar zakarun Turai.
Click to see content: Liverpool_top_scorers_hausa
Ta yaya za a kwatanta Salah da su Ronaldo?
Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo da Lionel Messi na Barcelona da kuma Neymar na Paris St-Germain su ake gani mafiya shahara a duniyar tamaula a yanzu, amma ta yaya za a kwatanta kwazonsu a bana da Salah?
Dan wasa Wasan da aka buga Kwallo Taimako a ci kwallo Nasara wurin kai hari Samar da damar cin kwallo Har da nuf rag

Salah 47 43 13 23.89 87 90

Ronaldo 39 42 8 16.22 53 111

Messi 50 40 18 14.81 112 12

Neymar 30 28 16 20.59 98


No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.