Bollywood : Jaruman India da suka yi mutuwar ban al'ajabi - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Bollywood : Jaruman India da suka yi mutuwar ban al'ajabi

<
Divya Bharti
'Yar kwalisar jaruma wadda tana daga cikin jarumai mata da suka yi tashe a shekarar 1990. Ta yi mutuwar bazata inda ta fado daga hawa na biyar a gidanta.'Yan sanda sun yi bincike a kan mutuwarta inda a karshe aka gano cewa kashe kanta ta yi. Sannan kuma akwai jita-jitar da ake yadawa cewa mijinta Sajid Nadiadwala ne sanadin muturta. Ta mutu a ranar 5 ga watan Aprilun 1993, tana da shekara 19. Ta fito a fina-finai kamar Deewana da Vishwatma da kuma Dil Ka Kya Kasoor.

2. Manmohan Desai
Darakta ne wanda ya bayar da umarnin fina-finai kamar Amar Akbar Anthony da Coolie da kuma Dharam Veer. An samu gawarsa ne bayan ya fado daga barandar gidansa. Rahotanni sun ce ya shiga damuwa ne bayan koma bayan da ya samu a sana'arsa, yayin da wasu kuma ke cewa ya gaji ne da ciwon bayan da ke damunsa, don haka ne ya kashe kansa. Ya mutu a ranar 1 ga watan Maris 1994.
Jia Khan ta fara fito wa ne a cikin fim din Nishabdh, sannan kuma ta fito a fim din Ghajini. An samu gawarta ne a rataye a jikin silin na rufin gidanta da ke Juhu a ranar 3 ga watan Yunin 2013. Mahaifiyarta ta ce ba kashe kanta ta yi ba, kashe ta akayi, inda ta zargi saurayin 'yar Sooraj Pancholi da alhakin mutuwarta, saboda tangardar da suka samu da saurayin nata. Ta mutu tana da shekara 25 da haihuwa.
Guru Dutt, jarumi ne kuma furodusa ne haka ma ya kan bayar da umarni. Ya yi fina-finai kamar Pyaasa, Kaagaz Ke Phool da Sahib Bibi Aur Ghulam da kuma Chaudhvin Ka Chand, wanda kusan fina-finai ne irin na da tun ba bu kala a ciki. An samu gawarsa ne sakamakon shan giya da kuma wasu kwayoyi da suka wuce kima. Guru Dutt dai na fama da matsalar damuwa. Ya mutu a ranar 10 ga watan Octoba, 1964, yana da shekara 39.
Parveen Babi, ita ce jarumar Indiya ta farko da ta fito a bangon mujallar Time Magazine. 'Jarumar ta yi fama da ciwon tabuwar hankali. An samu gawarta ne a gidanta da ke Mumbai. To sai dai kuma likitoci sun ce, binciken da aka yi a kan gano musabbabin mutuwarta ya nuna cewa cakawa kanta wuka ta yi. Parveen Babi ta yi tashe ne a fina-finan 70s, ta kuma fito fina-finai kamar Kaalia da Namak halaal da kuma Deewaar. Ta mutu tana da shekara 55 a duniya. Parveen Babi ta kasance 'yar gayu a lokacin da ta ke raye, kuma kusan fina-finanta da Amita Bacchan ta yi su.
6. Kunal Singh
Jarumin Indiya da ya fito a fina-finan Tamil. Matashi ne da ya fito a fina-finai kamar Dil Hi Dil Mein da Kadhalar Dhinam da kuma Punnagai Desam. An samu gawarsa ne a rataye a jikin sili a gidansa.To amma mahaifinsa ya ce ba kashe kansa ya yi ba, kashe shi aka yi. Ya mutu yana da shekara 30 a ranar 7 ga watan Fabrairun 2008.
Shahararriya ce a tashar mawaka ta MTV. Ta kashe kanta saboda ta samu matsalar soyayya. Ta fasa auren saurayinta Gautam Khanduja ne, saboda ya yi mata karyar cewa bashi da mata alhali kuma yana da ita. Nafisa ta kasance mai tallata kayan kawa, kuma ta taba lashe gasar sarauniyar kyau ta "Miss India Universe" a 1997, kuma ta samu shiga gasar Miss Universe ta duniya a Amurka a wannan shekarar. Ta mutu a ranar 29 ga watan Yuli 2004, tana da shekara 26.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.