Rundunar Sojin Kasa ta sanar da ranar kammala Rawar Mesa II - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Rundunar Sojin Kasa ta sanar da ranar kammala Rawar Mesa II

<
Hukumar Sojin Kafa na Najeriya ta ce za ta kammala Rawar Mesa karo na biyu a ranar 14 ga wannan wata
- Kwanel Sagir Musa ne ya bayar da wannan sanarwan
- Ita dai Rawar Mesa karo na biyu an fara ta ne a ranar Juma'a 15 ga watan Satumba na 2017
Hukumar Sojin kafa ta Najeriya ta tabbatar da cewan ranar 14 ga watan Oktoba na 2017 ne ranar da zata kammala salon aiki mai taken Rawar Mesa da ta ke gudanarwa a Kudu maso Gabashin kasannan nan.
Kwanel Sagir Musa, Mataimakin Daraktan sashin alakar soji da al'umma na rundunar Enugu, ya sanar da hakan. Sanarwar ta bayyana cewan kura ta lafa a duk wuraren da a baya ta tashi.
Rundunar Sojin Kasa ta sanar da ranar kammala Rawar Mesa II

Rundunar Sojin Kasa ta sanar da ranar kammala Rawar Mesa II
Ya kuma ce sakamakon yawaitan shawagi da sojin ke yi don tabbatar da tsaro, an samu kamo masu tada zaune tsaye da karbe makamai daga hannayen su.

DUBA WANNAN: Kiwon Lafiya: Hanyoyi 5 domin kare kamuwa da cutar dajin mama (Kansa)
Sojin sun samu nasara a lokuta mabambanta wurin kamo masu laifi irin su matsafa da barayin man fetur da masu 'yan sace-sace da masu safaran kwayoyi da sauran 'yan hayaniya.Sanarwar ta kara sa cewan akwai lokacin da soji suka samu nasarar kawar da gumurzu da ya kusan barkewa tsakanin kungiyon matsafa masu adawa da junan su.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.