Kannywood-Sakon maryam booth zuwa ga masoyinta - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Kannywood-Sakon maryam booth zuwa ga masoyinta

<
Jaruma Maryam Booth ta mika sakon soyayya da jinjinawa izuwa muradin zuciyarta a shafin ta na instagram domin taya shi murnar ranar haihuwa.
Jarumar ta bayyana masoyin nata a matsayin wadda ya raya zuciyar ta bayan mutuwar ta; kuma ta ayyanashi a matsayin wadda ya nuna mata soyayyar gaskiya. Ga sakon
"You stepped into my life and mended a broken heart. You stitched up my open wounds and showed me how to love fearlessly. For your birthday, I offer my sincerest gratitude for everything you do.happy birthday FUTURE"

KARANTA:- Kannywood -Rahama Sadau Ta Turawa Mawaki classic Sako
A cikin kwankin da suka wuce ne jarumar ta sanar cewa dalilin da yasa ba'a ganinta a film sosai shine laifin Producers da Directors ne, Jaruma Maryam Booth tana daga cikin jaruman da akayi hasashen haskawansu sosai a Kannywood dubi da yadda ta fara harkar da wuri da kuma zaman ta a gidan yan film.

Amma tun bayan dawowar ta daga kasar Malaysia inda taje karo karatu, sai yan kallo suka rage kallon jaruman a finafinai abunda yasa wasu suke tinanin kamar ta bar harkan. Jarumar de ta jima tana korafi akan zaben yan wasa (casting) inda take zargin ba’a yin abun akan cancanta da dacewa, sai akan wa ka sani wa ya san ka da son zuciya.
Ta rubuta a shafin ta na Istagram a inda take cewa “Ban taba barin Kannywood ba, kuma bazan bari Ba. Kada ku zarge ni da rashin fitowa a finafinai, ku zargi producers da directors”

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.