Friday, 13 October 2017

Dandalin Kannywood: Rayuwar dakin miji ta fi ta fim dadi - Fati Ladan


Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa a masa,antar Kannywood watau Fati Ladan ta kwarmatawa majiyar mu cewa rayuwar Auren da ta samu kanta a ciki ta fiye mata rayuwar fim din da tayi a shekarun baya dadi da muhimmanci. Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi wakilin majiyar mu a kwanakin baya kimanin shekaru hudu kenan bayan tayi aure ta rwdena sana'ar yin fim din.

Majiyarmu dai ta samu cewa jarumar a cikin firar ta kuma shawarci sauran jarumai mata na masana'antar fim din a wannan lokaci da su kame kan su su kuma maida hankali sosai wajen gudanar da sana'ar ta su saboda a cewar ta lokacin 'ya mace a masana'antar dan karami ne. Haka ma dai jarumar Fati Ladan ta bayyana kuma cewa a ra'ayin ta yawan da 'yan matan fim din ne suka yi musamman ma yara masu kananan shekaru yake jawo kuruciya da yawa a masana'antar. Fati Ladan dai ta yi aure ne kimanin shekaru hudu da suka gabata inda Allah ya azurta ta da samun da namiji amma daga baya ya rasu


EmoticonEmoticon