Law Gwamnatin tarayya na shirin yi wa yan Boko Haram shari'a a asirce - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Law Gwamnatin tarayya na shirin yi wa yan Boko Haram shari'a a asirce

<
Labaran da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni ne da cewa gwamnatin tarayyar Najeriya na shirin yin shari’ar wasu da ake zargin yan kungiyar nan ce ta Boko Haram ne a asirce ba tare da ba yan jarida damar halartar zaman kotun ba.
Mun samu dai cewa daya daga cikin manyan jami'an ma'aikatar shari'ar kasar ta Najeriya ne dai da bayaso a bayyana sunan sa ya shaidawa kamfanin dillacin labaran kasar Faransa hakan inda kuma ma har ya bayyana wasu dalilan da yasa za'ayin hakan.
Gwamnatin tarayya na shirin yi wa yan Boko Haram shari'a a asirce
Gwamnatin tarayya na shirin yi wa yan Boko Haram shari'a a asirce

Bestarewa.com.ng

 ta samu dai cewa jami'in ya ce gwamnatin ta yanke wannan sahawarar ne saboda dalilan tsaro da kuma rahoton da suka samu daga jami'an ta na farin kaya.
Idan mai karatu dai zai iya tunawa, a ranar 9 ga watan gobe ne ake sa ran fara shariar wadanda ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne da ke tsare a wuraren daban-daban kamar yadda muka ruwaito a makon da ya gabata.
Haka ma dai mun samu cewa kimanin yan kungiyar ta Boko Haram din sama da 1,600 ne za'ayi wa shari'ar a wannan lokacin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.