El-Rufai ya shara kuka bayan ya hadu da yaron da aka kwakwulewa idanu - BESTAREWA BlOG

Header Ads

El-Rufai ya shara kuka bayan ya hadu da yaron da aka kwakwulewa idanu

<


Gwamnan Jihar Kaduna ya ga abin da ya sa shi kuka a yau
– Malam Nasir El-Rufai ya zubar da hawaye ne dazu a Zaria
– Hakan ya faru ne bayan ya hadu da yaron da aka cirewa idanu

Yau an ga wani bangare na Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai inda ya rusa kuka yayin da ya hadu da wani yaro da matsafa su kayi wa illa a Makarantar Yahaya Hamza da ke Zaria.
El-Rufai ya shara kuka bayan ya hadu da yaron da aka kwakwulewa idanu

Mai Rusau ya rusa kuka dazu a Zaria
Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna yayi kuka har da hawaye yayin da ya je rabawa yara kayan aiki dazu a wata Makaranta a cikin Garin Zaria. Gwamnan ya kai ziyara ne Makarantar da yaron yake wanda aka gyara aka kuma raba wasu na’urorin karatu a Yau Laraba.

El-Rufai ya shara kuka bayan ya hadu da yaron da aka kwakwulewa idanu

El-Rufai ya shara kuka bayan ya hadu da yaron da aka kwakwulewa idanu" width="1200" />
Gwamnan Kaduna El-Rufai yana kuka
El-Rufai yayi kukan ne bayan ya hadu da yaron da wasu matsafa su ka zakulewa idanu kwanakin baya mai suna Sadiq Usman wanda ke da shekaru 5 kacal a Duniya. Gwamnan ya buge da kuka a gaban Jama’a yayin da yaron ya zauna a kan cinyar sa har ta kai yana share hawaye da tsumma.
Kwanaki kun ji cewa mai girma Gwamnan Jihar Kadunan Malam Nasir El-Rufai ya kai ta’aziya ga iyalin Abidu Yazid wanda aka sace surukar sa aka yi garkuwa da ita bayan an kashe mijin ta

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.