[Labari Da Dumi Duminsa] Shugaba Buhari zai dawo Najeriya don bikin babban Sallah – Shahararriyar jarida - BESTAREWA BlOG

Header Ads

[Labari Da Dumi Duminsa] Shugaba Buhari zai dawo Najeriya don bikin babban Sallah – Shahararriyar jarida

<
An rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo Najeriya don bikin babban Sallah

- Uwargidansa ta soke shirinta na tafiya aikin hajji

- An rahoto cewa likitocinsa basu amince da shawarar ba

An sanya dawowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa lokacin bikin babban sallah a cewar jaridar Sahara Reporters.

Shugaban kasar na wajen kasar sama da kwanaki 100 don ganin likita a birnin Landan sannan kuma a cewar jaridar yanar gizo, wasu na kusa da shin a shirin dawo da shugabna kasar nan da makonni biyu don bikin babban sallah wato Eif-il-Kabir.

An rahoto cewa uwargidan shugaban kasar, Aisha Buhari ta soke tafiyarta aikin Hajji domin ta kasance a kusa lokacin dawowar shugaban kasar gida Najeriya.

An yi zargin cewa hakan ya saba ma umurnin likitocin dake kula da shugaban kasar yayinda suke son ci gaba da kasancewarsa a chan na wasu makonni hudu.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.