Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019 - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019

<
-Jami'iyyar PDP tana son tsaya da Attajiri Aliko Dangote a matsayin dan tarar ta na shugabancin kasa a zaben 2019
-Jami'iyyar ta aike da tawaga domin zawarcin attajirin dan kasuwan
-Jami'iyyar PDP tana sa ran Dangote yayi takarar shugaban kasa a karkashin tutar jami'iyyar
Bisa ga dukkan alamu, jami'iyyar PDP tana niyyar tsayar da babban attajirin dan kasuwan nan da yafi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote a matsayin dan takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa.
Rahoton jaridar Daily Times yace PDP tana shirye-shiryen zawarcin attajirin dan kasuwan domin yayi takara a jami'iyyar.
NAIJ.com ta tattaro cewa jami'iyyar zata tsaida dan Arewa ne a matsayin dan takarar shugaban kasa sannan shugabancin jami'iyyar zata koma sashin kudu.
Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019
Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019
Wata majiya a jami'iyyar PDP tace ziyarar da jami'iyyar aka kai ma Alhaji Aliko dangote bazai rasa nasaba ta yi masa tayin tsaya wa takarar shugabancin kasa a karkashin tutar jami'iyyar.
Majiyar tace tuni an ma riga an aike tawagar da zata je zawarcin Aliko Danote, an yanke shawaran hakan ne bayan kwamitin jami'iyyar wanda ta hada da tsohon shugaba Goodluck Jonathan sun tattauna kuma suka yarda cewa shine ya dace yayi musu takara.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.