Kaji dafa'in da wannan katon yake anfani da wajen yi wa yara fyade - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Kaji dafa'in da wannan katon yake anfani da wajen yi wa yara fyade

<
Wani katon asara da ke da shekaru a kalla 32 a duniya mai suna Ayuba Salihu a yau din nan Alhamis ya bayyanawa hukumar nan dake kare hakkokin yara ta jihar Neja irin dafa'in da yake anfani da shi wajen yi wa yara fyade.
Salihu wanda dubun sa ta cika ya shaidawa hukumar cewa ita wannan yarinyar da yayi wa fyade mai shekarun da basu wuce 8 a duniya ba yayi anfani ne da Naira 100 kacal wajen jan ra'ayin ta ne.
Kaji dafa'in da wannan katon yake anfani da wajen yi wa yara fyade
Kaji dafa'in da wannan katon yake anfani da wajen yi wa yara fyade
 ta samu cewa Salihu ya bayyana cewa ita dai yarinyar ya ganta ne a gaban shagon sa tana ta kuka da kuma ya tambaye ta meye matsalarta sai ta shaida masa cewa kudin ta ne suka fadi sai shi kuma ya bata sannan daga bisani yayi anfani da ita.
Da take bayar da ba'asi, kakar yarinyar ta shaidawa hukumar cewa a ranar da bun ya faru ta aike ta ne ta siyo mata abu a shago tun safe amma bata dawo ba sai can wajen karfe 9 na dare. Da muka binciki inda taje shine take shaida mana dukkan abun da ke faruwa a tsakanin su.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.