Fadakarwa Ta Sa Ni Shiga Harkar Fim Din Hausa - Inji Wata Jaruma - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Fadakarwa Ta Sa Ni Shiga Harkar Fim Din Hausa - Inji Wata Jaruma

<
Babban burina shi ne na zama tankar Hadija Gabon, a harkar fim baya ga ilimantarwa da zan yi ta harkar, inji matashiyar jaruma Amina Yola.
Ta ce ta shiga harkar fim domin sana’a ce da take burge ta mussaaman ma yadda suke fadakar da jama’a abubuwan da suke faruwa na yau da kullum.
Matashiyar ta bayyana cewa bata shiga harkar fim ba sai da ta karbi izini daga wajen iyayenta , inda ta ke cewa harkar fim harka ce da sai an hada da hakuri, ganin cewar ana mu’amala da mutane da dama.
Amina ta ce tun daga garin Yola ta zo Kano, ta kuma sayi form din shiga sana'ar bayan kammala bincike aka bata gurbin karatu.
Kawo yanzu dai ta ce ta cimma burinta, tunda ta shiga harkar kuma abinda ranta ke so Kenan. daga karshe ta ce a duk iya lokacin da take cikin wannan masana’anta bata fuskanci wata matsala ba.
-Naij

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.