Duniya Mai yayi inda ranka kasha kallo Wani mutumi dan Najeriya ya kama wata irin kifi yayin gina rami a Yenagoa (hoto) - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Duniya Mai yayi inda ranka kasha kallo Wani mutumi dan Najeriya ya kama wata irin kifi yayin gina rami a Yenagoa (hoto)

<
A cikin wani sakon da ya riga ya yadu a kafofin watsa labarun, wani saurayi ya bayyana yadda ya sami wata kifi mai ban mamaki yayin da yake gina rami a Yenagoa, Jihar Bayelsa.

Wani mutum na Najeriya ya sa mutane cikin mamaki a kan wata hoto da ya yada a kafofin watsa labarai na kifin da ya gino daga wani rami.

A cewar wani sakonshi a shafin sa na Facebook, Emmanuel Emmanuel Udoh, yana yin aikinsa na gine-gine a lokacin da ya ga kifin da ya kamata yana cikin ruwa.

Wani mutumi dan Najeriya ya kama wata irin kifi yayin gina rami a Yenagoa (hoto)


Har yanzu Udoh yana tambayar idan kifin ya komo bushashshiyar ƙasa saboda gurbatar ruwan kogi.

Emmanuel ya ce "Kafin inyi tambaya ko za'a iya cin wannan kifin, ina mamakin abinda yasa kifi zai bar cikin ruwa ya dawo inda babu ruwa.

Shin yana iya yiwuwa cewa ruwa mai zurfin ya lalace sosai ta hanyar binciken man fetur ne, shi yasa ya dawo cikin wuri mai tsabta ko kuwa ikon Allah ne kawai?, Yanzu wannan za'a iya cin shi? saboda akwai su dayawa anan wurin".

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.