Ban san wa ke biyan kudin jinyar Buhari ba - Femi Adesina - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Ban san wa ke biyan kudin jinyar Buhari ba - Femi Adesina

<
Buhari na da iko Najeriya ta biya masa kudin jinya

- Channels TV: Ya kamata a fito fili a fadi wa ke biyan kudin kowa ya sani

- Buhari ya kusa dawowa

Mai bawa Shugaba Buhari shawara a harkar kafofin yada labarai da ganawa da al’umma, Femi Adesina, a ranar litinin yace bai san wa ke biyan kudin jinyar Buhari a birnin Landan ba. Mista Adesina ya fadi haka ne a shirin gida talabijin din Channels, "Siyasa a Yau".Shugaba Buhari da Femi Adesina

Shugaba Buhari ya tafi jinya tun 7 ga Mayu.

Mista Adesina yace kuma bai kamata sai an damu a san wa ke biya ba.

“Ya kamata al’umma su sani don shine shugabansu,” mai gabatar da shirin, Seun Okinbaloye, yake fadawa Adesina. “Shin daga asusun kasa ake biyan kudin?”

“Ban san wa ke biya ba, amma Buhari yana da hakki asusun kasa ya biya masa kudin jinya a ko ina.”

Mista Adesina yana cikin wadanda suka kai wa Buhari ziyara a Landan a karshen satin da ya gabata.

“Mun sami shugaba Buhari garau, cikin hankalinsa da barkwancinsa, kuma jiki yayi sauki. Amma ba zai iya dawowa ba sai likitocinsa sun ce masa lokacin zuwa gida yayi."


Makiya Buhari suna ta jefa magana a kan kwanan Buhari 100 baya kasa, kuma har sun fito sun yi zanga-zanga a kan ko ya dawo gida ko kuma yayi murabus daga kujerar mulki. Mabiya bayansa kuma sun ce ai kan ya tafi ya mika ragamar mulki zuwa mataimakinsa Osibanjo, kuma a kundin tsarin mulki ba’a sa ga iyakacin lokacin da shugaba zai iya yi ba a kasar waje.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.