Wednesday, 23 August 2017

Bahaushiya musulma ta farko da ta kai matakin kwamanda a Najeriya (hotuna)

Bahaushiya musulma ta farko da ta kai matakin kwamanda a Najeriya (hotuna)
Hajara ta fara aiki a matsayin jami’ar soja a 1986. Ta samu daukaka inda ta kasance bahaushiya kuma musulma ta farko daga yankin arewa da ta fara kai wa matsayin kwamanda, wanda yayi daidai da matsayin kanal a soja. Hajara, yar marigayi Marafan Birnin Kudu, Kanall Bashari Umaru daga Birnin Kudu a jihar Jigawa, yanzu ita ce shugaban ma’√°ikatan jinya na asibitin sojoji dake Kano. Ta taba zuwa yaki a Congo, daga cikin wuraren da tayi aiki akwai Ibadan da Kaduna. An haife ta ne a Dorayi Quarters a ranar 19 ga watan Maris, 1964, ta girma ne a Yakasai Quarters a Kano, sannan ta fara karatun firamare a Wagwarwa Primary School, sannan ta koma St. Louis Primary School.
R ead more: Shugaba Buhari ya kashe zama da Ministocin sa na yau
Kasancewarta daliba mai ilimi, Hajara ta samu shiga Queen’s College, Lagos da St. Louis Secondary School, Kano. Ta zabi karatu a Kano ne saboda sauyin aikin da mahaifinta ya samu zuwa Kano. Bayan ta kammala da karatun sakandare ne ta shiga makarantan koyon jinya a Kano.
A cikin makarantan ne ta yanke shawarar shiga aikin sojojin sama wanda ya biyo bayan neman kwasan ma’aikatan kula da lafiya.
‘’Babu shakka hakan ya kasance abun al’√°jabi. Mahaifiyata bata so hakan ba ko kadan. Mahaifina ya amince ne kawai domin faranta mun rai. Amman ya karfafa mun gwiwa, ya kuma girmama zabin da nayi." Inji ta.


EmoticonEmoticon