ANA BIKIN DUNIYA AKE NAKIYAMA Zahra Buhari da Mijinta sun je Kasar Spain domin taron ranar haihuwa - BESTAREWA BlOG

Header Ads

ANA BIKIN DUNIYA AKE NAKIYAMA Zahra Buhari da Mijinta sun je Kasar Spain domin taron ranar haihuwa

<
Iyalan gidan Indimi sun tashi zuwa kasar Spain don bikin ranar haihuwar biyu daga cikin su

- Mai makudan kudin ya kai shekara 70 tare da 'yar sa da ta cika shekara 29,kuma duk iyalansa sun halarta

- Zahra da Ahmed Indimi sun halarci wurin

Idan akwai abin da Indimi suka iya yi sosai,shine zuwa kasashe daban-daban na duniya don jindadi. Idan kana kusa dasu dole kaji sha'awan kusancin su, babu kuma kamar yanayin hada taron ranar haihuwar su.


Zahra Buhari da Mijinta sun je Kasar Spain domin taron ranar haihuwa.

Dukan 'iyalan Indimi sun tsere don bikin ranar haihuwar biloniya Indimi na shekara 70, har da 'yar sa Adama Indimi da tayi nata na shekara 29 kwana biyu da suka wuce. Dukan iyalan sun kasance a wurin, ciki harda sabuwar memba na iyalan, Zahra Buhari. A yanki mai kyaun gaske na Spain.

Zahra wanda ta riga ta saba da harkokin tafiye tafiye na iyalan Indimi ,ta kasance a wurin tare da Mijinta,Ahmed Indimi yayin da suka yi bikin ranar haihuwar Adama wanda ke da matashi mai shekaru 29 da haihuwa.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.