Wata sabuwa anatinani Boko Haram tamutu ashe likimo sukayi Sun sake sabuwar hanya kai hari - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Wata sabuwa anatinani Boko Haram tamutu ashe likimo sukayi Sun sake sabuwar hanya kai hari

<
Wasu na tunani 'Yan Boko Haram sun dawo da karfin su

- Kwanan nan dai an yi rashin Sojojin Najeriya kusan 40

- Haka kuma an sace wasu Malaman Jami'ar Maiduguri

Yanzu haka wasu na tunani 'Yan Boko Haram sun dawo Jihar Borno da karfin su don kuwa barnar da aka yi kwanan nan har a cikin Garin Maiduguri.Boko Haram ta sace Malaman Jami'ar Maiduguri

An dai yi asarar Sojojin Najeriya 41 sannan kuma an sace wasu Malaman Jami'ar Maiduguri da kuma Direban su. Wadannan mutanen dai su na aikin hako mai ne a Yankin na Maiduguri wanda hakan ta sa aka tsaida aikin hako man har sai harkar tsaro ya gyaru.

KU KARANTA: 'Yan Borno sun soki Gwamnatin TarayyaWani hari na Boko Haram a 'yan kwanakin nan

Mun samu labari cewa an samu gawa akalla 48 na mutanen da Boko Haram su ka kashe a asibiti Jami'ar Maiduguri. Har yanzu dai Gwamnati ta gaza fadin asalin mutanen da aka rasa wajen harin na Boko Haram.

Jiya dai Ministan ilmi ya kai ziyara Maiduguri inda yace ba za a rufe Jami'ar ba. Matakin da aka dauka na tsaida aikin hako mai a Arewacin Najeriyar ya jawo batutu a mutanen na Maiduguri.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.