NDLEA takama wani mutum Mai kimani shekara 59 a filin jirgin malam Aminu Kano dauke da kwayoyi - BESTAREWA BlOG

Header Ads

NDLEA takama wani mutum Mai kimani shekara 59 a filin jirgin malam Aminu Kano dauke da kwayoyi

<
Jami’an hukumar NDLEA sun kama wani mutum dauke da miyagun kwayoyi a filin jirgin sama na Aminu Kano

- An samu mutumin da miyagun kwayoyi mai nauyin kilo 25 a jakar ta sa

- Hukumar NDLEA ta ce ta fara bincike a kan mutumin da ake zargi da aikata laifin

Jami’an bincike na hukumar NDLEA a cikin filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano sun kama wani mutum da ke sana’ar kamun kifi kuma mai shekaru 59 da haihuwa, Mista Chukwuani yayin ƙoƙarin wani shiga jirgin kamfanin kasar Habasha zuwa Johannesburg, Afirka ta Kudu ta hanyar Addis Ababa da wasu miyagun kwayoyi.

An samu wannan mutumin da ake zargi da miyagu kwayoyi mai nauyin kilo 25 a cikin jakarsa bayan da aka riga aka tantanceshi.

Kamar yadda bestarewa.com.ng ke da labari, babban kwamandan hukumar NDLEA a filin jirgin sama ta Kano, Mista Ambrose Umoru ya ce an kama Chukwuani ne a filin jiran shiga jirgi dangane da wani rahoton sirrin.

Filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano

Tuni jami’an hukumar NDLEA sun shiga bincike wannan bawan Allah domin gano daga inda yake sayar miyagun kwayoyin

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.