Musha Dariya - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Musha Dariya

<
Daga .............

😂😂MUSHA DARIYA😂😂

Wani saurayi ne a makaranta, ya shiga dakin karatu (library) da shigarsa sai ya hango wata kyakkyawar budurwa a gefe zaune ita kadai, kun san halin samari da son hulda da 'yan mata masu kyau, gogan naku sai ya isa inda take yai mata sallama, sai yace mata na ganki ke kadai zaune, shine naga bai dace kyakkyawar mace kamarki ta zauna cikin kadaici ba, shine nace bari na zo na tayaki hira, kawai sai budurwar ta daga murya da karfi  tace "KA GA MALAM NI BA 'YAR ISKA BA CE DA ZAKA CE IN BIKA DAKINKA IN KWANA KAJE CAN KA NEMI 'YAR ISKA IRINKA" gaba daya hankalin mutanen dake wurin ya dawo kansu, saurayin yaji kamar kasa ta tsage ya shige ciki don kunya,
bayan mintuna kadan sai budurwar tazo inda yake tayi kasa da murya tace masa ina karatun psychology ne na iya karantar abinda ke ran mutum, ko ban tambayeka ba na san kaji kunya da abinda nayi ma, saurayin shima sai ya buda bakinsa da karfi yace "KWANA DAYA A DUBU HAMSIN (50000) GASKIYA SUNYI YAWA, HALA AN FADA MAKI SATA NAKE YI?" gaba daya hankalin mutanen wurin ya sake dawowa kansu, wasu suka dinga yi mata dariya suna cewa ashe duk kanwar ja ce, saurayin ya kalleta shima yayi kasa da murya yace mata karki damu ina karatun law ne na sanin  hanyoyin kama mutum idan yayi min laifi.😂😂😂😂😂😂😂

Don Allah A Cikinsu Wa Yafi qwarar Wani?

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.