Labaran chikin kasa - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa

<
-Nayi matukar mamaki da suka yi watsi da muhimmin kudiri irin wannan

-Wannan ranar bakin ciki ne ga jam’iyyar mu

-Kada APC manta da amanar da mutane suka bata

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jigo jama'iyyar APC, Atiku Abubakar, ya zargi mambobin jam'iyyar dake majalisar dattijai da cin amana sabo da kin sauya fasalin kasan dan kai wa mutane cigaba daga biranai har karkara.

A wani jawabi da aka fiitar daga offishin sa na Abuja, Mista Abubkari yace senatocin APC sun yi watsi da babban dama da za su yi amfani da wajen cika alkwaran da jam,iyyar ta dauka na kawo wa mutane canji

Atiku ya zargi Sanatoci APC da cin amana don ƙin sauya fasalin kasa

“Dakatar da dokan sauya fasali da senatocin APC sukayi cin amanana ne ga jam’iyyar da kuma alkawaran da ta dauka lokacin yakin neman zabe."

KU KARANTA: Ana tuhumar hadimin sarkin Musulmi akan badakala

“Nayi matukar mamaki da suka yi watsi da muhimmin kudiri irin wannan na yiwa kasa garanbawul. "

“Wannan ranar bakin ciki ne ga jam’iyyar mu. Amma ina da tabbacin APC za ta koya darasi daga wannan matsalar da ta ja ma kanta kuma ta tunan amanan da jama’a suka bata."

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.