Labaran chikin gida Nigerian a yau muka samu sakon ziyara EFCC gidan tsohon gwamna kashim shettima - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin gida Nigerian a yau muka samu sakon ziyara EFCC gidan tsohon gwamna kashim shettima

<
 Hukumar EFCC ta musanta labarin kai samame gidan gwamnan jihar Borno

- A karshen makon data gabata ne aka dinga watsa labaran cewa EFCC ta kai samame gidansa

Hukumar yaki da almundahana da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta musanta batun dake yamamadidin cewa sun kai wata samame a wani gidan gwana Kashim Shettima dake garin Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Kaakakin hukumar Wilson Uwujaren yana bayyana hakan a ranar Lahadi 30 ga watan Yuli, inda yace hukumar bata da wata masaniya dangane da samamen da ake ikirarin ta kai. “Bamu da wata masaniya dangane da hakan.” Inji shi.Majiyar bestarewa.com.ng ta samu wasu rahotanni masu tushe daga karkashin kasa dake tabbatar mata da cewa “Babu wani samamen bincike da muka kai gidan Kashim, amma sai gashi wasu na yada labarum karya da hotuna wai tare da ICPC muka kai samamen.


Kashim Shettima

“Kunga kuma bama aiki tare da ICPC, ban da haka, gwamnoni da mataimakansu, na da kariya daga ire iren wannan samame kamar yadda shugaban kasa da mataimakinsa suke dashi." Inji majiyar.

Ku biyo mu a

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.