Sahihin magani ulcer fisabillahi - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Sahihin magani ulcer fisabillahi

<

. SAHIHIN MAGANIN ULCER FISABILILLAH
*Saboda Watan Ramadan Mai Albarka
Ga duk mai fama da wannan larurar ta ulcer koda tayi tsanani zai samu waraka da yardan Allah.
A samu Bawon Kankana a busar dashi bayan ya bushe sai a daka ya zama gari a samu kamar kimanin Gwangwanin madara Peak na ruwa daya na garin bawon da aka daka sai a samu garin hulba cokali 3 da garin habbatu sauda cokali 3 da da garin tafarnuwa Rabin cokali sai a hadasu waje guda bayan an hadasu waje daya sai fara sha.
YANDA AKE SHAN MAGANIN HANY UKU CE.
* HANYA NA FARKO ZAKA SAMU ZUMAR KA LITTER DAYA DA RABI A JUYE MAGANIN A CIKI, A JUYA SAI A DINGA SHAN COKALI 3 SAU 3 A RANA KAFIN ACI ABINCI DA MINTUNA 10.
* SAI HANYA TA BIYU KUMA A DINGA ZUBA COKALI DAYA A RUWAN DUMI DA ZUMA COKALI 3 A SHA KULLUM SAU UKU KAFIN ACI ABINCI.
* SAI HANYA TA UKU SABO DA MASU CIWON SUGA ZASU SAMU MADARA SU DINGA SHA A CIKI.
Don Allah ayi kokarin yadawa (Sharing) domin 'yan'uwa su amfana, albarkar wannan watan. Allah ya bada lafiya...

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.