RAMADAN KAREEM - BESTAREWA BlOG

Header Ads

RAMADAN KAREEM

< *YAYA MATSAYIN AZUMIN WANDA BAYA SALLAH, SHIN YANADA AZUMI?*

الحمدلله.

Amsa:Wanda baya sallah ba'a karbar aikinsa na azumi ko zakkah ko hajji, ko duk wani aiki.

Imamul bukhari yaruwaito hadisi (520) daka buraida yace: Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace:( Duk wanda yabar sallar la'asar hakika ya rusa aikinsa).

Ma'anar yabata aikinsa shine yarushe bazai amfaneshi ba, wannan hadisi yanuna wanda baya sallah ba'a karbar aikinsa, wanda baya sallah bazai amfana dakomai na aikin saba, aikinsa baza'a kaishi zuwa ga Allah ba.

Ibnul qayyeem rahimahullah yace: dangane da ma'anar wannan hadisin acikin littafinsa Assalah (65)

" Abunda yabayyana acikin hadisin, barin sallar iri biyune,barin sallah na har abada shi kwata kwata bayayi wannan yana bata aikinsa gaba daya, da kuma barinta na wani lokaci kamar wuni guda sananne wannan yana bata aikinsa na aiya wannan yinin, Barin sallah gaba daya shike lalata aikinsa gaba daya, barinta na wata rana yana bata aikin wannan ranar ko ranakun dabaya sallar.


An tambayi shaik usaimin acikin fatawarsa (87) game da hukuncin azumin wanda baya sallah.

Saiya amsa; Wanda baya sallah azuminsa ba ingantacce bane ba karbabbe bane, domin wanda baya sallah kafirine wanda yayi ridda saboda fadin Allah madaukakin sarki:

فإن تابوا وأقموا الصلاة وآتوا الزكوة فإخوانكم في الدين.  التوبة/ 11

Idan sun tuba sun tsaida sallah sunbada zakkah to sunzama 'yan'uwanku a'addini.

Dafadin Annabi sallallahu Alaihi wasallam ( Banbanci  dake tsakanin musulmi dawanda bashiba shine yin sallah wanda yabar sallah hakika yakafirta) Turmuzi ( 2621) Albani ya ingantashi acikin sahihu turmuzi.

Saboda kuma shine maganar sahabbai gaba dayan imma baizama ijma'insu akaiba, Abdullahi bin shaqeeq rahimahullah yana cikin tabi'ai wadanda suka shahara yace: Sahabbai sunkace basa ganin wani aiki cikin ayyuka wanda barinsa kafircine inba sallah ba, abisa wannan idan mutum yai azumi kuma baya sallah to azuminsa anmayar masa baza'a karba masaba, kuma bazai amfaneshiba ranar alkiyama, zamuce dashi yi sallah sannan kai azumi, amma kai azumi baka sallah azuminka ba karbabbe bane za'a mayar maka saboda kafiri ba'a karbar duk wata ibada tasa.

An tambayi malaman lajnatul da'imah ( 10/140) tambaya kamar haka:idan mutum yakanyi kwadayin yin azumi kuma yana sallah da azumi amma kuma dazarar azumi yawuce shikenan yadena sallah, shin yana da azumi?

Sai suka amsa: sallah rukunice daga cikin rukunan musulunci muhimmai wanda daka kalmar shahada sai ita, tana cikin farillai na tilas wajibi, duk wanda yabar sallah yana maikore wajabcinta ko kuma saboda wulakantata ko saboda kasala hakika yakafirta, amma masu azumi suna sallah acikin azumi kawai wadannan suna yaudarar Allah ne,tir da mutanen dabasu san Allah ba sai awatan azumin ramazhaan, azuminsu bai ingantaba tare dabarin sallarsu alokacinda ba na azumi ba, sudin kafiraine kafirci babba, koda basu kore wajabcin sallar ba amafi inganci maganganun malamai.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.

🌙Tambayoyin Musulunci🌙

+


🌙MARHABA🌹 RAMADAN🌙

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.