Musha Dariya mu more abin mu - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Musha Dariya mu more abin mu

<
Wani mahaukacine!!!!🚢🏿! yazo wucewa, sayyaga ana zaman makoki, sai ya zauna akayi addu,a dashi, bayan angama sai ya tambaya, macace ko namiji, sai akace masa namiji,  sai yace babbane ko karami, sai akace masa yaro ne, abinka da gogan naku sai yace allah shikara,πŸ˜‚πŸ˜‚ watakilma dashi ake tsokanata.
πŸ˜ƒπŸ˜„πŸ˜‚πŸ˜‚

Wani Danfulani ne yaje saudiyya sai Allah yayimasa cikawa a can da aka bugowa dan uwansa waya aka fadamasa sai yace ai dama nasan za'ayi haka Kana gidanka Allah yakasheka Balle kaje gidanshiπŸ˜„
 Asha DariyaπŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…            Wani bafulatani ne aka saida shanun shi biyu a kayi Mashi aure,ranar da yazo gida zaya ga amaryar shi sai yaga babu shanun shi sai yace baffa Ina shanu na sai yace ai sune aka saida a kayi maka aure,sai ya fara fada yana cewa sai an biya shi shanun shi akace yayi haquri ya shiga dakin amarya ansan yanda za'ayi,bafulataninka ya shiga dakin amaryar shi ya kwana safiya nayi ya fito a guje yace baffa a Saida sauran shanun aqaro mani mata......πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…
 Wani bafillace ne mahaifinsa ya rasu sai mutane suka zo zaman makoki anata gaisuwa shi kuma sai ya koma gefe daya ya yi tagumi yana ta tunani daya daga cikin masu ansar gaisuwa sai ya lura da halin da yake ciki sai ya zo gurinsa yana ba shi haquri yana cewa ka yi haquri ai duk mai rai mamaci ne budar bakin bafillacen nan sai ya ce ni ba mutuwa baffa nake kuka ina tuna tambayoyin nan da wanakiri zai yi ma baffa shi kuma baffa ga shi da zuciya........
: Mu Shakata.............

Danfulani yaje sallah juma'a bayan yadawo sai yahadu da wani abokinsa. Sai abokinsa yace danfulani kasamu sallah, sai danfulani yace Eh Nasamu Daya Dakyar itama da ace natsaya Alwala da bazan samu ba....hhhhhhhπŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„

Wani saurayi ne yake son er gidan wani me kudi alhali bshi d sana'ar kirki, ita kuma budurwar bata damu da rashin kudinsa ba. Ana haka kwasam ya samu aiki ranar daya fara daukar albashi dubu shabiyar (15,000 ) bai xarce ko ina ba sai gidansu budurwarsa ya tambyeta ta fada masa abinda tafiso domin yau ya fara daukar salary (albashi) sai tace masa ba komai saida ya takura tace to su tafi super market suna xuwa ta dau man shafawa irin wanda take amfani dashi a gidansu.. sai yace ta qara wani abun tace sam ya ishe ta, sai ya wuce gurin biyan kudi akai calculating kudin man  duba sha hudu da dari biyar (14,500) canjinsa ya rage 500.. akace wane suna xaasa a reciept sae yace kawai sa MARIGAYIπŸ˜‚πŸ˜‚!!6

 Wani Saurayi ne mai suna aliyu clever suka hada appointment da Budurwar sa cewa zai zo gidan su ya dauke ta su fita shakatawa. Yana zuwa sai aka yi rashin sa'a,Babanta yana gida. Sai budurwar tayi caraf ta cewa saurayin: "Yauwa Allah ya sa ka taho min da littafin nan na ''Speak to me in English, my father doesn't understand" Sai saurayin yace: "kash! Sai dai kuma jiya na bada shi aro, amma na taho miki da "How is our outing going to be?" Sai budurwar ta ce: "To shi ke nan, amma dai na fi bukatar "wait for me under the tree outside Saurayin yace "to gobe in Allah ya kai mu zan aiko miki, har da "don't stay long pls." kafin saurayin ya fita sai baban budurwar yayi caraf yace: "To ka hado mata da " I understand everything you said" mana. 'Yan iska marasa kunya sai ki fita na gani. Hahahahaha πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„ don't laugh alone pls share it to your friends

 Dariya doleπŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€
Kuturu da makaho
Wani kuturune yaje bara a wata rumfar kasuwa, yana cikin barar sai ga wani makaho shima ya iso yana tasa barar. Can sai wani mutum ya taso ya raba musu naira d'ari biyar-biyar, ashe Kuturu yaji haushin abin da akayi.
Sai kuwa ya kalli makaho yace, banza kawai! Da bakaxoba dani  za'a ba duka, d'an bakin ciki kawai."
Sai makaho yace kai matsa can dan Allah! Kaine banza, tunda babu ma sunanka a cikin alkur'ani, koh akwaine?
Sai kuturu ya fusata yace,  walmasakina ta ubankace?  Kaine ma ai ba sunanka a cikin alkur'ani.
Sai shima makahon ya fusata yace, walakad mananna ta ubankace?"πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

‬: πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ Labarin Dan Nigeria πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜‚ Wani Dan Nigeria ne yaje Kasar waje Sai 'yan Sanda suka Biyoshi       zasu Kamashi. Sai ya shiga wani gidan Rawa, Suka rasa yanda zasuyi su kamashi. Sai wani Bature yace, " Kun San yanda Zakuyi?" Sukace " A'a. " Sai yace, " A kashe duk wutar  dake wurin tayi kamar minti ukku." Sai kuwa aka kashe, bayan Minti ukku yace," A kunna. " Ana kunnawa abinka da dan Nigeria, Sai yace " NepaaaaπŸ˜€!!!" Baturen yace," Gashi can, Ku kama shi." lol πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.