Saturday, 3 June 2017

LABARI DA DUMINSA

Tags

A Najeriya an bada rahotan sake bullar cutar murar Tsuntsaye wato Bird Flu a wasu jihohi biyar na kasar.
Jihohin sun hada Kano da Kaduna da Bauchi da Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma Jihar Filato.
Wani jami'i mai kula da lamarin a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar ya shaida wa wakilinmu cewar an samu bullar cutar a jihar ne a gonaki uku.
Sakataren kungiyar masu kiwon kaji a jihar Kano, Umar Kibiya, ya tabbatar da bullowar cutar kuma ya ce cutar ta karya jarin manoma da dama a shekarar 2015 inda har yanzu suna jiran kudin diyyyan da gwamantin kasar ta yi alkawarin biyansu domin su koma kiwo.
Cutar wacce da hanzari kan kashe Kaji musamman a gidajen gona ta haifar da asara mai yawa ga masu gidajen gona a jihohi da dama a Najeriya a shekarar 2015, inda har yanzu wasu masu kiwon kaji ke cewa ba a biya su diyyar da gwamnati ta yi alkawarin biyan su ba.


EmoticonEmoticon