An Kai hare hare abirin london - BESTAREWA BlOG

Header Ads

An Kai hare hare abirin london

<
An kai wasu jerin hare-hare a birnin Landan inda 'yan sanda suka ayyana "lamarin ta'addanci."
'Yan sanda dai sun bayyana jerin hare-hare a matsayin wani abu da ke kan gudana.
Daga farko dai wata farar motar daukar kaya ce ta buge masu tafiya kan gadan Landan wadda ke tsakiyar birnin inda ya kashe wasu tare da raunata wasu.
Wani wakilin BBC da ke kan gadan a lokacin da lamarin ya faru ya ce motar ta buge mutane shida ko biyar bayan ta kama hanyar mutanen da ke tafiya kan gadan na Landan.
'Yan sanda sun ce adadin wadanda aka kashe kan gadan na Landan ya fi daya.
'Yan sandan sintirin Birtaniya sun ba da sanarwar wasu mace-mace bayan wannan harin inda suka ba da sanarwar wani lamari wanda ake kyautata zaton ya danganci motar daukar kaya da wuka.
Rundunar 'yan sandan birnin Landan ta tabbatar da wani dauki na makami da aka kai kasuwar Landan inda aka ba da labarin caka wa mutane wuka.
'Yan sandan sun ce an yi harbe-harbe, kuma daga bisani suka ce an ayyana wadannan hare-hare a matsayin ayyukan ta'addanci.
Yanzu haka dai an kai wasu mutanen da suka ji rauni otel din Andaz Hotel da ke kan layin Liverpool inda akwai karin 'yan sanda masu makamai.
An rufe asibitin Guy da ke kusa da wurin domin kare ma'aikata da marasa lafiya kamar yadda aka yi da asibitin St Thomas da kuma asibitin yara na Evelina da ke da nisa mil daya daga wurin.
An tura wasu 'yan snada anguwar Vauxhall, amman daga baya jami'ai sun ce lamarin daba wuka ne wanda ba shi da alaka da hare-haren gadan Landan da kasuwar Borough.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.