Saturday, 19 January 2019

Hausa music ::: shamsu alale jini jikina

Music :::   Sabuwar wakar Shamsu Alale mai suna ” Jinin Jikina ” wannan wakar ta musammance domin nishadantar da ku masoya nasan kunsan shmasu alale wajan wakar soyayya.
GA KADAN DAGA BAITIN WAKAR:-
– Kinzam jinin jikina
– A zuci na rike
– So ya wuce kwatance zan miki inuwa
– Kauna tana da dadi in kayi dace
Kinsa inata kaudi akanki nace
– Sufar farin masoyi yazan na mance
– Shassheka so yasani tamkar na zamma gawa
– Mai nazari cikin so baiyi da wasa
– in zuci ta amince so baiyi ginsa

                 DOWNLOAD MUSIC HERE

Friday, 18 January 2019

Labaran siyasa ::: Saura kwana 28 zaben 2019: Bayani kan 'yar takara Obiageli Ezekwesili

Obiageli Ezekwesili tsohuwar mataimakiyar shugaban Bankin Duniya ce, sannan kuma ta rike mukaman ministan ilimi da kuma ma'adanai a Najeriya.
Sabanin sauran manyan 'yan takara, Mis Ezekwesili kirista ce wadda ta fito daga yankin kudancin Najeriya, kuma jam'iyyar da take yin takara a karkashinta karama ce idan aka kwatanta da tasu.
Ta jagoranci kamfe na Bring Back Our Girls wanda ya ja hankalin duniya baki daya bayan da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace 'yan mata dalibai 300 daga garin Chibok na jihar Borno da ke Arewa maso gabshin Najeriya.
Oby Ezekwesili ta shirya karawa da Buhari a zaben 2019
'Ya kamata a yi bayani kan asusun Nigeria'
Masana na ganin cewa kwarewarta kan tattalin arziki baiwa ce ga Najeriya sai dai rashin goyon baya daga manyan 'yan siyar kasar ka iya kawo mata tsaiko.
Ta yi alkawarin cewa in dai aka zabe ta za ta sauya fuskar tattalin arzikin Najeriya daga dogaro da man fetur da kuma samar wa matasa aikin yi.
"Yar shekara 55, Mis Ezekwesil tana hankoron zama shugabar kasa mace ta farko a Najeriya duk da cewa abu ne mawuyaci a kasar da maza suka yi kaka-gida.

Labaran chikin kasa :: an bada Berlin Dino melaye abisa wasu sharadda

Kotu ta bayar da belin Dino Melaye bayan ya kwashe kwanaki a hannun 'yan sanda
- Sai dai kotun ta bukaci ya gabatar da mutane 3 da za su karbi belinsa kuma ciki har da magatardar majalisar tarayya
- Kotun ta bayar da belin sanatan ne domin ya samu cikaken kulawa daga likitocinsa kafin a gurfanar dashi
Wata babban kotu da ke Maitama a babban birnin tarayya Abuja ta bayar da belin Sanata Dino Melaye da halin yanzu ya ke tsare a asibitin rundunar 'yan sanda da ke Abuja.
Da duminsa: Kotu ta bayar da belin Dino Melaye
Alkalin kotun, Justice Yusuf Halilu ya bayar da belin saboda dalilan rashin lafiyar da sanatan ya ke fama dashi kamar yadda lauyan Dino Melaye, Mike Ozekhome ya shaidawa kotun a takardan neman belin.
Alkalin yana ganin Dino Melaye ba zai iya fuskantar shari'a ba idan bashi da lafiya kamar yadda The Nation ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Sabon IG ya bayyana babbar matsalar da aikin dan sanda ke fuskanta a Najeriya
Ya ce tunda ba za a iya gurfanar da sanatan a kan gadon asibitin ba ya dace a bashi beli domin ya samu ya murmure.
Alkalin ya bukaci sanatan ya gabatar da mutane uku da za su karba belinsa, daya daga cikinsu kuma ya kasance magatakardan majalisar tarayya wadda zaiyi alkawarin gabatar da shi a kotu a duk lokacin da ake neman shi a nan gaba.
Ya ce sauran mutane biyun da za su karba belinsa kuma su kasance sun mallaki filaye ko gidaje a Abuja.
Ku biyo mu domin karin bayani ...

Labaran siyasa ::: Maine dalilin xuwa atiku amurka

A yau Juma'a dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a Najeriya, Atiku Abubakar, ya kai ziyara Muryar Amurka inda ya mayar da martani kan kalaman da gwamnatin Najeriya ta yi dangane da zuwansa Amurka.
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce gwamnatin Najeriya ta tsorata da ziyarar da ya kai Amurka yana mai nuna cewa ziyarar ba ta masu dadi ba.
Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne a zamanin mulkin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai Sashen Hausa na Muryar Amurka a yau.
Yayin kuma wannan ziyara ta Atiku, rahotannin daga Najeriyar sun nuna cewa, gwamnatin kasar ta ce ba damuwarta ba ne idan Atiku ya je Amurka,
A lokacin da yake ganawa da manema labarai a yau, Ministan yada labarai, Lai Mohammed ya ce abin da suke jira shi ne Atiku ya dawo ya zo ya amsa tambayoyi kan hannun da ake zargin yana da shi a durkushewar bankin kasar.
Wasu dama na ganin ziyarar ta Atiku a Amurka za ta kawo karshen tababar da aka jima ana yi ta cewa, ba zai iya zuwa Amurka ba, domin yana gudun hukumomi za su kama shi.
Kafafen yada labaran Amurka kuma sun yi nuni da cewa, da alamu gwamnatin Amurka ta yi na'am da dan takarar.
Amma a nasa bayanin, Atiku ya ce koda gwamnatin Amurka na goyon bayan wani dan takara, ba za ta taba nunawa a fili ba.

Hausa hip hop music ::: R.C TOP FT 2KAPO FT JAHUKCY AMANA

Music :: Hausa hip hop music daga arewa hip hop R.C TOP FT 2kapo ft jahukcy amana           DOWNLOAD MUSIC HERE

Hausa music ::: Isah Ayagi -Ameenah

Music :::  Sabuwar wakar Isah Ayagi mai suna ” Ameenah ” domin nishadantar da masu suna ameenah da kuma masoya ameenah, kawai kubiyo kuji wakar.
GA KADAN DAGA BAITIN WAKAR:-
– Anayi gobe zamu gana dake ameena
– Cikin dare na kasa bacci sabo da murna
– Baru nake gari ya waye akan idona
– Ni dake mu gaisa ameena
– Ki tambayen na baki amsa Ameena
– Na baki tabbaci na kauna Ameena


 

              DOWNLOAD MUSIC HERE

Zaman takewa :: wane abubuwa akeso mata Susa Dan gyran jiki da xaisa fatarsu tayi kyau da laushi da santsi

Da farko dai kafin ki fara kwalliya akwai bukatar NATSUWA sannan akwai bukatar LOKACI ina nufin wadataccen lokacin da zai isa a awaitar da kwalliya daki-daki kuma a tsare don tabbatar da cewar an yi kwalliyar a natse ba wai kawai a yi ta gara babu ba. Don haka ki tabbatar duk abun da zai dauke maki hankali kin gama da shi.
Abu na biyu kuma shine ki san yanayin fatarki tun daga launinta zuwa gautsi, tauri ko laushinta. Wannan zai ba ki damar sanin ababen kwalliya da za ki harhada wadanda fstarki za ta karba. Saboda sau tari za ka ga wasu sun yi kwalliya amma sam kwalliyar ba ta zauna akan fatarsu ba. Ga yadda za ki gane yanayin fatarki:
YADDA ZA KI GANE YANAYIN FATARKI
Fata mai maiko (OILY SKIN): ko da yaushe za ki ga fatar jikinki tana da maiko ko kin shafa mai ko kirim ko ba ki shafa ba. Kuma da kin goge zuwa wani lokaci za ki ga fatar na nason maiko sannan kuma da kin yi kwalliya za ta narke ta lalace ki yi ta kyalli fauu.
YADDA ZA KI KULA DA FATA MAI MAIKO (OILY SKIN)
Rika yawan yin FACIAL MASK da kwai: Yadda ake yin facial mask na kwai. Za ki fasa kwanki danye, sai ki cire kwanduwar ki bar farin, sai ki rufe fuskarki da tishu fefa (tissue paper), sai ki yi amfani da blusher (wani burushi na shafa kayan kwalliya) ki na dangwalar ruwan kwan kina shafawa a tishu fefar da ki ka lullube fuskarki da ita har sai kowane bangare na fuskar ta ki ta jike da ruwan farin kwan. Za ki bar shi na tsawon mintuna 10 zuwa 15 sai ki wanke da ruwan dumi.
2. Hanya ta biyu na magance maikon fuska ita ce yawan goge fuskarki da lemon zaki ko lemun tsami kafin shafa kayan kwalliya. Yana da kyau ki san cewa yin amfani da nikakkiyar farar shinkafa ki jika ta cikin madara kana ki cuda kafatanin jikinki da ita akalla mintina 20 kafin ki shiga wanka ba wai kawai magance maikon fuska ya ke ba, a’a, hadin na sanya laushi da shekin fata. A kula in ki ka yi wannan hadin ba kya bukatar wanka da sabulu, sai dai akwai bukatar ki yi amfani da ko dai ruwan sanyi ko na dumi wajen dirje jikinki da kyau ta yadda kwabin zai wanku sosai.
3. Hanya ta uku na magance maikon fuska ko fata gaba daya ita ce ki kasance duk man shafawa ko kirim din da za ki saya ya zama an rubuta FOR OILY SKIN (Domin masu maikon fata) ko kuma FOR ALL SKIN TYPES (Domin kowace irin fata) ba wai kawai kamshinsa ya maki dadi ba ko kuma dan shi ake yayi ba ko dan wance ta siya ko yana da tsada ba
A darasi na gaba za mu yi magana akan wani nau’in fata da yadda ake kula da shi kafin daga bisani mu yi bayani akan yadda ake daura musu kwalliya.
Sai dai zan dan yi karin bayani kan yadda za ki wanke fuskarki tare da cire tishu fefar da ki ka lullube fuskarki da ita a yayin da ki ka yi facial mask (kamar yadda na yi bayani a mataki na farko na magance maikon fuska). Ga yadda ake yi: Za ki wanke fuskar da ke lullube cikin tishu faifa da ruwan kwai ne da ruwan sanyi. Sa’annan wankan da za ki yi a lokacin ya zama da zallar sabulu babu soso kuma ya zama da ruwa mai zafi sosai. Sai a wanka na biyu ne wanda watakila da yamma ko da rana za ki yi shi, sai ki yi da soso da sabulu kuma da irin ruwan da ki ke da bukata, ko dai na sanyi ko kuma na dumi.
Wata hanyar har ila yau, ita ce ta hanyar nika bawon lemon zaki ya niku lukwui. sai ki kwaba garin da madara kwabi mai dan kauri. sai ki shafe hadin a fuskarki ki bar shi har na tsawon mintuna 10-15 kafin ki wanke da ruwan sanyi. Wannan ita ma wata hanya ce ta magance maikon fatar fuska.
A darasinmu na yau kuma za mu yi duba ne akan yadda za ki magance matasalar bushewar fata domin ita ma busasshiyar fata tana bada matsala ga nagartacciyar kwalliya.
BUSASSHIYAR FATA: Za ki iya gane busasshiyar fata ce da ke da wadannan alamun: Saurin bushewar fata a lokacin iska ko dari, yawan yi saba, kyasfi, fashewan lebe a lokacin iska ko dari, yawan jin kaikayi da kasancewar fata ta yi fururu kamar an bada miki garin fulawa, yamutsewar fata da sauransu. Ko shakka babu irin wannan fatar ta fi kowace iriyar fata bukatar gyara, kuma wannan darasi ya zo mi ki da hanyoyin magance matsalar bushewar fata.
Hanyoyin Magance Matsalar Bushewar Fata
 • ki daina wanka da ruwa mai zafi domin yana taimaka wa wajen tatse maikon da ya saura gareki
 • ki daina zama a cikin rana mai zafi
 •  kayan sawarki ya kasance mai laushi ba mai gautsi ba
 • ki daina yawan barin jikinki ko wani bangare na jikinki a bayyane musammam a lokacin iska
 • Lebenki ya kasance a kodayaushe ya kasance cikin mai ko basilin ko lip gloss mara kala. Ki kiyayi jambaki na wani dan lokaci ko kuma daga kin gama abun da za ki yi da Jambakin ki goge ki sa lip gloss dinki
 • idan za ki yi burushi da safe ki wanke har da labbanki domin za su yi laushi kuma mataccen fatar leben zai fita. Sai dai ba a goga burushin da karfin tsiya
 • ki dinga yawan shafa madarar yoghurt a fuskar ki ko madara idan ta bushe, sai ki dauraye da ruwan sanyi sosai
 • kada ki rika yawan durje fuskarki kuma kada ki yawaita amfani da Sabulu da yawa
 • ki rika yawan amafani da mayuka da aka yi su da dan itaciyyar APRICOT  ko kuma ya kasance da akwai shi a ciki musamman ma ga kanki
 • ki sayi OATS ki nika shi ya yi laushi sosai idan za ki yi wanka sai ki dibi chokali daya ki zuba a kofi daya na ruwan zafi ki juya idan ya narke sosai sai ki zuba a ruwan wankanki juya da kyau (ruwan wankanki ya zama shi ba mai sanyi ba kuma ba mai dumi ba.
 • Idan kin gama kada ki goge jikinki ki bari fatarki ta shanye ruwan jikin naki.
 • Avocado (piya) ki cire bawon ki yar sai ki dama ta yi laushi ki shafeta a fuskar (kina lailaya fuskarki a hankali) idan ya bushe ki dauraye da ruwa mai sanyi sosai
 • ki raba ruwan wankan ki biyu, idan kin gama wanka da daya sai ki shafa basilin (vaseline) ko man kade sannan ki watsa sauran ruwan a jikinki. Za ki sake shafa mai in kin fito
 • ki yawaita shafa wa fuskar ki da hannu da kafarki mai duk bayan kowace salla domin sun fi komai bushewa a jikinki
 • idan za ki shafa mai a fuskarki, bayan kin lakato man a hannunki kin mutsuttsika sai ki fara tafa hannunki duk biyun akan fuskar ki a hankali ko ta ina har sai man ya shafu a haka
Kwalliya A Lokacin Zafi
Ko kun san cewa kwalliya da ababen maiko bai dace ba a wannan lokacin? A wannan lokaci ne fitowar kuraje kamar su pimples da blackheads babu wahala a sakamakon irin maikon da fuska ke tarawa.
Idan ana son kulawa da kurajen fuska da kuma hana wasu fitowa, ga wasu shawarwari da ya kamata a bi:
•Hoda; Idan za a yi amfani da hoda a tabbata cewa hodar ba ta da maiko. A yi amfani da hodar da za ta tsotse gumin fuska. Kuma ana amfani da kala mara duhu domin ta haskaka fuska.
•Ana amfani da prima kafin a dora hoda a fuska. Shi prima yana hana kwalliya bacewa da wuri, wato yana dan rike kwalliya.
•Kamar yadda a wannan lokacin ba za a so sanya bakaken kaya ba ko kuma kaloli masu duhu, haka fuskar ma ba komai za a shafa mata ba, sai a samar mata kala mai haske. Kada kuma a manta shafa hoda mai haske a kan hanci.
•A rage amfani da janbaki mai maiko domin zafin rana na sanya shi narkewa kuma hakan na bata kwalliya sosai.
•Kada a manta idan za a yi amfani da gazal ko kayan kwalliyar fuska, kamar su mascara da sauransu a yi amfani da wadanda idan ruwa ya taba ba zai bata kwalliya ba.
Yadda Ake Kwalliyar Fuska
Mata da dama musamman ma wadanda za su yi aure sukan biya kudi mai yawa domin a yi musu kwalliyar fuska. Ba shakka daga an ga wanda aka yi wa wannan kwalliya lallai za a ce kwalliya ta biya kudin sabulu. Ina so in sanar da ku cewa wannan kwalliyanr za a iya yin ta a gida idan akwai kayan aiki.
Da farko dai ana so a wanke fuskar da sabulu sannan a jira ta bushe kafin a shafa mata komai.
•Ana so a samu ruwan goge fuska (cleanser) a goge fuskar da shi da auduga.
•Bayan an yi hakan, sai a shafa man SPF (sun protection fuemula).
•A samu hodar fandesho dai-dai kalar fatar mutum sannan a shafa.
•A samu hoda haka a sake shafawa.
•Sannan sai a samu reza ga wanda ke da cikan gira sai a aske shi kadan.
•A samu gazal din mac guda biyu; daya baki daya kuma ba baki sosai ba sannan a zana girar da shi.
•Bayan haka sai a samu ‘concealer’ da na ‘eye shadow’ da burushin ‘eco tools’ da burushin ‘eyeliner’.
•Sai a fara taje giran da burushin ‘eyeliner’
•Sannan sai a zana girar da gazal din mac da dayan mara baki sosai a hada su.
•Bayan an shafa sai a sake taje su da ‘eyeliner brush’ din.
•Sai a dauko ‘brush sigma E65’ a debi eye shadow mai duhu a sake shafawa a girar.
•A sake dauko gazal din a sake zana giran sama da kasa.
•A shafa ‘concealer’ din da ‘brush E65’ din dai-dai kalar fatar mutum.
•Sannan sai a shafa ‘eye shadow’ kalar kayan da za a saka.
•Sai a shafa jan baki.
Hanyoyin Kulawa Da Fuskarki
Wanke fuska kafin ki kwanta bacci a kowane dare:
 
Me ya sa ya kamata a rika wanke fuska kafin a kwanta barci?
 
Na san kowa zai so ya ji amsar wannan tambaya. Wanke fuska na da matukar muhimmanci ga mace da namiji. Mata da dama ba su damu da yin wanka da daddare kafin su kwanta barci ba. Wata ma tun kwalliyar da ta yi da daddare ta fita hira wajen saurayinta haka za ta shigo gida ta kwanta barci ba tare da ta wanke fuskarta ko kuma ta yi wanka ba. Don haka ya kamata ki canza, ki rika wanke fuskarki kafin ki kwanta barci saboda:
 • Wanke fuska ko wanka kafin a kwanta na sanya kwanciyar hankali da samun barci mai dadi.
 • Idan mutum ya kwanta ba tare da wanke fuska ba, mayukan da ya shafa a fuskarsa na taruwa su fitar da manyan kuraje, inda sai an yi da gaske kafin a rabu da su.
 • Yana da kyau a wanke fuska da sabulun wanke fuska, domin fuska ba ta cika kwari ba kamar sauran fatar jiki.
 • Kada a manta a rika goge fuska da sinadarin ‘cleanser’ kafin a kwanta barci.
 • Ki yi amfani da ‘cleanser’ da ta dace da fatarki kafin a fara amfani da ita wajen wanke fuska.
 • Rashin wanke fuska kafin a kwanta na rage wa mace kyau, domin idan kurajen suka feso a fuska kan samu matsala ko ta canza.
 • Rashin yawan wanke fuska na janyo maruru a fuska.
 • Rashin wanke fuska ko wanka na janyo fitowar kyasbi a fuska, don haka sai a kiyaye.
Yadda Ake Amfani Da Madara Wajen Magance Maikon Fuska
Shan madara na kara lafiyar jiki, tana sanya fata ta rika sheki, ta sanya ta yi taushi da kuma santsi. Hakan ya sa a yau Mujallar Alummata ta kawo muku yadda ya kamata ku yi amfani da madara wajen magance yawan maikon fuska.
Abubuwan bukata
 • Madara
 • Gishiri
 • Ruwa
 • Auduga
 • Zuma
Amfanin madara wajen magance maikon fuska
1. Madara na goge daudar fuska: A samu madara rabin kofi, sannan a hada ta da rabin cokalin gishiri, sai a sanya ruwa a gauraya har sai gishirin ya narke. Daga nan a shafa a fuska da wuya zuwa minti 2 ko 3 kafin a wanke da ruwan dumi.
2. Madara na sanya fata santsi: don haka za a iya amfani da ita a matsayin sinadarin ‘cleanser’. Da farko a samu auduga, sai a tsoma a cikin madarar ruwa, daga nan a rika goge fuska da ita. Daga nan a jira ta bushe kafin a wanke.  Yin hakan na rage maikon fuska, kuma zai sanya fuska ta yi taushi da santsi.
3. Za a iya amfani da madara don kara wa gashi karfi: musamman lokacin sanyi da gashi yakan tsinke. A zuba madara a kan gashi a cuda har ta taba tsagun kai, sai a jira na minti kadan kafin a wanke. Yin hakan na kara karfin gashi kuma yana hana shi tsinkewa.
4. Za a iya hada madara da zuma sannan a shafa a fuska. Yin haka na hana tsagewar fatar fuska saboda sanyi.
 

Labaran siyasa :: ta faru ta kare mai yasa atiku abubakar yaje kasa amurika

Karshen dai tika-tika-tik. Bayan cece- kucen da aka rinka yi a Najeriya akan cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Abubakar ba zai iya shiga Amurka ba, a karshe dai ya shiga.
'Yan Najeriya musamman dai 'yan jam'iyya mai mulki ta APC sun ta kalubalantar shi a kan cewa idan ba tsoro ba yaje kasar Amurka.
Atiku Abubakar dai tsohon mataimakin shugaban kasa ne a Najeriya kuma a yanzu haka dan takarar shugabancin kasar ne a karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta PDP.
Buhari da Atiku: Amurka da EU na son a rungumi zaman lafiya
Najeriya ta bai wa Amurka shawara kan Atiku Abubakar
Zaben Najeriya: An soma fafatawa tsakanin Atiku da Buhari
Sau da dama ana ta rade-radin cewa idan Atiku yaje Amurka zai fuskanci dauri sakamakon wani laifi da ya tafka a kasar.
Ya sha dai musanta wannan zargin a lokuta da dama inda ya bayyana cewa babu wanda ya taba kama shi da laifin aikata rashawa.
Tirkashi, ana wata ga, ga wata. Mulki ta bar arewa ta yamma ta koma arewa ta gabas. Allah ya nuna mana mulkin @atiku .
— Atikulated2019 (@Utchay_dbold) 17 Janairu, 2019
Malam @BashirAhmaad a gaya wa baba @MBuhari da magoya bayanshi fa. Shugaba mai jiran gado
@atiku ya isa DC, saura #AsoRock Bijahi Nabiyul Ummi (SAW)
— khalifa (@usmanwaziri2) 17 Janairu, 2019
Wannan photoshop/hade-hade ne ni ban yarda yaje ba in kuma yaje to yakamata mu ganshi tare da wani babban baamurke
— Dahiru Ahmad Ali (@DahiruAhmadAli1) 18 Janairu, 2019

Sai dai a ranar Alhamis 17 ga watan Junairu ne kwatsam aka ga hotunan Atiku suna yawo a shafukan sada zumunta wadanda ke nuna cewa ya je Amurka.
An dai ga tsohon mataimakin shugaban kasar ne tare da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a cikin hotunan.
Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, yana ziyara a Amurka ne domin ganawa da manyan jami'an gwamnati da 'yan kasuwan kasar da kuma 'yan Najeriya mazauna Amurka.
Sai dai a wata hira da Atiku ya yi da BBC a kwanakin baya, ya bayyana cewa ya nemi izinin shiga Amurka, amma an hana shi.
Ko da aka tambaye shi a kan batun gidansa na Amurka da aka yi gwanjonsa sai ya bayyana cewa gidan matarsa ne da ya saya mata a kasar kuma ita ta sayar da gidan nata.
A hirar dai ya bayyana cewa ba dole ba ne sai mutum ya je Amurka kafin ya zama shugaban kasar Najeriya, babu inda aka fadi haka a kundin tsarin mulki, in ji Atiku.
Tun bayan isar Atiku Amurka, tuni dai mutane da dama suke sharhi suna tafka muhawara a shafukan sada zumunta akan wannan batu.
Da dama wasu daga cikin magoya bayansa a shafukan sada zumunta suna ta murna a kan cewa gwaninsu ya shiga Amurka, wasu kuma har yanzu ba su yarda ba inda suke ganin cewa kamar hada hotunan aka yi.

Naija music ::: DMW ft. Davido, Zlatan – Bum Bum

Music :::   DMW ft. Davido, Zlatan – Bum Bum
Ahead of Davido’s upcoming concert, ‘ Davido Live at the 02 Arena’ , London slated for 27th January.
Davido Music Worldwide premieres a brand new single titled ‘ Bum Bum ’ featuring label Boss,
Davido and rave of the moment, Zlatan.
YOU MAY LIKE: Casanova – 2AM ft. Tory Lanez & Davido
The Rexxie produced single steers up the atmosphere and guarantees what his fans should expect on his upcoming concert. The song suites the Zanku dance pattern.
Finally, the video to ‘Bum Bum’ has been shot, directed by DMW in-house director,
Twitch . Out shortly!!
Listen, download and share your thoughts below.

               DOWNLOAD MUSIC HERE

Naija music :: GoodGirl LA – Bless Me

Music :::  Sitting at home, a night before her biggest performance of 2018, GoodGirl
LA caught a hook and immediately recorded a voice note then sent it to her manager. That 40 seconds hook became her performance intro, and soon people
started to ask for a full record.
‘Bless Me’ is an aspirational song about a young girl, who’s waiting on a big break. It was produced by Quebeat.
handles: @iamgoodgirlla
Enjoy.

                   DOWNLOAD MUSIC HERE

Hausa hip hop & R & B music :: Eddy Kool – Sojojin Arewa Ft. 2flash Da D.O.A x B.O.G x Dr Pure

Music ::: Eddy kool of the renowned VibesNation decides to dish out this hard hitting hiphop joint ‘Sojojin Arewa’ Eddy kool enlist the creative lyrical ability of Dr Pure , featuring 2flash Da D.O.A x the lyrical B.O.G.
             DOWNLOAD MUSIC HERE

Labaran siyasa ::: Kuri’un Buhari bana sai sun zarce abin da ya samu a 2015 – Gwamnan Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu yayi alkawarin ganin cewa jam’iyyar APC ta samu gagarumar nasara a zaben da za ayi kwanan nan. Saura dai makonni 4 yanzu rak a gudanar da zabe a kasar.
Atiku Bagudu yace Buhari zai samu makukun kuri'a a jihar sa
Mai Girma Atiku Bagudu ya sha alwashin ganin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya tashi da tarin kuri’un da ba a taba samun su ba a fadin jihar. Bagudu yace abin da Buhari zai samu a zaben bana sai ya haura kuri’un sa na zaben 2015.
Sanata Atiku Bagudu na jam’iyyar APC yayi wannan jawabi ne a wajen wani kamfe da Mai dakin sa watau Dr. Zainab Shinkafi Bagudu ta shiryawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin garin Birnin Kebbi a tsakiyar makon nan.
KU KARANTA: Kan Malaman addini ya rabu a game da zaben Buhari da Atiku
Gwamnan ya fadawa dubban jama’an da su ka halarci wannan taro na yakin neman zabe cewa Buhari zai tashi da kuri’un da bai taba samun su ba tun da yake takara a jihar. Buhari yana neman zarcewa ne wannan karo a kan mulki.
Gwamna Atiku Bagudu dai ya yabawa irin gayyar da Matar sa Zainab Shinkafi Bagudu ta tara a jihar. Gwamnan yace dandazon jama’an da su ka fito wajen kamfen din ya nuna yadda matasa da mata ke tare da shugaban kasa Buhari.
Idan ba ku manta ba, a zaben 2015 da aka yi, shugaba Muhammadu Buhari ya samu kuri’u sama da 560, 000 ne yayin da jam’iyyar da ke mulki a lokacin watau PDP ta tashi da kuri’u kusan 100,000 rak.

Thursday, 17 January 2019

Labaran afirka :: Bayan Kashe Wani Dan Jaridar Ghana-'Yan Jaridar Kasar Sun Ce Yanzu Aiki Yake

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun harbe suka kashe wani dan jaridar Ghana da ya kware a buga labaran da suka shafi abin fallasa kuma ma’aikacin kamfanin jarida na Tiger Eye PI mai suna Ahmed Hussein Suala, a unguwar Madina dake birnin Accra.
Suala yana cikin ‘yan jaridar nan da suka bankado wasu ayyukan cin hanci da rasahawa a hukumar kwallon kafa ta Ghana, lamarin da ya rutsa da shugaban hukumar Kwesi Nyantakyi. Ahmed Suala ya taka muhimmiyar rawa a cikin wannan binciken fallasa kuma hakan yasa ya yi bakin jini a wurin wasu da lamarin ya shafa.
Wani dan majalisar dokoki mai wakiltan mazabar Assin North a jihar Tsakiyar Ghana, Kennedy Agyepong yana cikin wadanda suka nemi a kaiwa marigayin hari a duk inda aka same shi. Dan majalisar ya zargi Ahmed Suala da kamfanin Tiger Eye da shisshigi a cikin rayuwar mutane, lamarin da ya kai ga dan siyasar fitar da hoton Suala a kan telbijin, wanda ‘yan jaridar suka ce makaminsu ne hukokinsu da suka rufewa a duk inda suke.
Kisar Ahmed Hussein Suala ya janyo suka da zargi a kan dan siyasar saboda bayyana huskar dan jaridar. Mutane da dama ne suke zargin Kenney Agyepong cewa yana da masaniya a kan kisar, saboda alkawarin da ya dauka a baya a kan telbijin cewa zai biya duk wanda zai samu Ahmed Hussein Suala ya ci zarafinsa. Kuma tuni ‘yan sanda sun gayyaci dan majalisar don yi masa tambayoyi.
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo Addo ya jajantawa iyalan marigayin kuma da kakkausar murya ya yi tir da wannan danyen aikin kuma ya kira ma’aikatar ‘yan sandan Ghana ta gaggauta kamo wadanda suka yi wannan aika-aikar.
Ita ma kungiyar ‘yan jarida ta kasar Ghana ta bakin shugabanta Affail Mooney, ta yi Allah wadai da wannan kisar ta kuma kwatanta kisar da babban bala’I ga aikin jarida a Ghana. Anas Aremeyaw Anas shugaban kamfanin Tiger Eye PI da marigayin ke aiki karkashinsa, ya lashi takobi cewa wannan kisar da zata sa su yi shuru ba, zasu ci gaba da aiki.
‘Yan jarida a Ghana sun bayyana kaduwarsu ga wannan danyen aiki da ba a saba gani a cikin kasar kana sun yi kira ga hukumomi su tashi tsaye su kare ‘yan jarida. Haka zalika ‘yan Ghana sun yi amfani da shafukan sada zumunta wurin bayyana alhininsu ga wannan kisar.

Labaran siyasa ::: mai yayi zafi haka

Kamfanin sada zumunta na Facebook yace zai fadada damammaki ga 'yan siyasa su tallata manufofi da tsare-tsaren su, yayin da a hannu guda kuma kamfanin ke daukar tsauraran matakan dakile yunkurin yin amfani da kafar sa wajen yada kalaman batanci a tsakanin 'yan siyasa.
Baya ga haka, kamfanin na Facebook na kokorin bullo da tsauraran matakai ta hanyar kimiyyar fasaha domin kare kutsen bayanai musamman a lokutan zabe a kasashe daban-daban na duniya,
A zantawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Daraktar kula da harkokin siyasa da cibiyoyin ketare ta kamfanin na Facebook, Katie Harbath tace yanzu haka kamfanin ya zabi Najeriya, da India, da Ukraine da kuma kasashen dake karkashin kungiyar Turai domin aiwatar da sabon tsarin.
Dr. Abbati Bako, masanin kimiyyar siyasa ne da harkokin sadarwa a fagen dimokaradiyya, yace kasar India ita ce dimokradiyya mafi girma a duniya, inda manyan ‘yan siyasa zasu iya amfani da shafin na Facebook wajen tallata manufofinsu saboda yawan masu amfani da shafin.
Shi kuwa Malam Abdulganiyu Rufa'i, kwararre akan fasahar dakile kalaman batanci ta kafar sadarwar zamani, yayi karin bayani ne dangane da sabbin matakan kamfanin Facebook. Yace a matakin Najeriya sun nuna cewa zasu yi kokari su ga sun tabbatar da cewa ba a yarda dan wata kasa ya sanya wata tallar siyasa ba sai dai ‘yan Najeriya da kansu, kuma zasu yi kokarin dakile duk wani labarin da ake hasashen ba na gaskiya bane.
Dangane da batun kutsen bayanai kuwa, akwai masu ganin cewa, mizanin ci gaban fasahar sadarwa da Najeriya keda shi bai kai a yi mata kutse ba ta hanyar kwamfuta.
Haka zalika, kwararren ya yi tsokaci kan yadda kamfanin na Facebook ka iya tsaftace tallikan 'yan siyasa kafin su kai ga abokan mu'amalar sa.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da wata kotun majistire dake Kano ta yanke hukuncin zaman kaso na shekara guda babu zabin tara akan wani matashi mai suna Mustafa Jarfa, bayan tabbatar da laifin kalaman batanci ta kafar sadarwa ta Facebook ga mataimakin gwamnan Kano Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna

Labaran siyasa ::: Atiku Abubakar Ya Gana Da Wadansu ‘Yan Majalisar Dokokin Amurka

Dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyar hamayya a Najeriya PDP, Alh Atiku Abubakar yana ziyara a Amurka inda ya gana da wadansu ‘yan majalisar dokokin kasa, yayinda a yau yake shirin zuwa ma’aikatar harkokin wajen Amurka
A cikin hirarshi da Sashen Hausa, jim kadan bayan fitowarshi daga majalisar dokokin Amurka, Alhaji Atiku ya bayyana cewa, ya tattauna ne da ‘yan majalisar kan abubuwan da suka shafi Najeriya da kuma dangantakar da Najeriya take so ta karfafa tsakaninta da sauran kasashen duniya, musamman Amurka.
Alhaji Atiku wanda yace ya zo Amurka ne bisa gayyatar wadansu kungiyoyi dabam dabam, ya kuma bayyana cewa, yana shirin kai ziyara ma’aikatar harkokin wajen Amurka inda zai tattauna da wadansu jami’ai, daga nan kuma ya gana da ‘yan kasuwa.
Dan takarar na jam’iyar PDP yace ziyarar tasa a Amurka manuniya ce cewa, babu gaskiya a cikin abinda ake fadawa mutane game da shi, yace ziyarar da ya kawo zata kara farfafawa wadanda har yanzu suke da shakku cewa, bashi da wani tabon da ya hana shi zuwa Amurka.
Ya bayyana cewa, Amurka a shirye take ta marawa kowacce kasa da take bin tafarkin damokaradiya baya, sabili da haka ya hakikanta cewa, tana tare da Najeriya a kokarin kasar na kare damokaradiya.

Labaran siyasa ::: Cikakken bayani kan rayuwar Shugaba Buhari na Najeriya

Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Muhammadu Buhari mai shekara 76 - mutum ne da ake ganinsa a matsayin tsayayye wanda ba ya gudu ba ja da baya.
Duk da shan kaye da ya yi a zabuka uku da suka gabata, amma ya sami nasara a zaben 28 ga watan Maris din 2015, inda ya zama dan adawa na farko da ya sami galaba a kan shugaban da ke kan karagar mulki.
Buhari ya kara da Shugaba Goodluck Jonathan, wanda dan yankin Neja Delta ne, a karo na biyu da gudanar da zaben.
A wannan karon ya yi sa'ar samun goyon bayan gamayyar jam'iyyun siyasar Najeriya mai suna All Progressives Congress (wato APC).
Buhari ba ya karya -Ministar kudi
Na zama 'Baba go slow' saboda dimokuradiyya - Buhari
Jam'iyyar APC ta sami karin karfi bayan da manyan 'yan siyasa daga jam'iyyar Shugaba Jonathan ta People's Democratic Party (wato PDP) suka sauya sheka, jam'iyyar ta PDP ce ta mamaye fagen siyasar Najeriya tun karshen mulkin soji a shekarun 1999.
Sa rai da samun sauyi
Bayan da shugaban ya dare mulki a 2015, 'yan Najeriya da dama sun saka rai da samun sauyin rayuwa, ta bangaren ingantuwar tsaro da tattalin arziki da magance cin hanci da rashawa.
Sai dai masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun sha cewa shugaban bai yi wani abin a zo a gani ba ta bangaren tattalin arziki.
Sai dai ana yaba masa ta wajen magance rikicin Boko Haram, duk da cewa suna ganin da sauran rina a kaba a wannan fannin ma.
A bangaren tattalin arziki kuwa, masu sharhi da dama suna ganin babu wani cigaba da aka samu, "sai ma kara tabarbarewa da yake yi."
Rashin lafiya
Shugaba Buhari ya shafe tsawon lokaci yana jinya a shekarar 2017, inda har ya shafe sama da kwana 100 yana jinya a Birtaniya.
Wannan al'amari ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a ciki da wajen kasar.
A lokacin da rudani ya yawaita kan halin da shugaban ke ciki da kuma rashin jin ta bakin makusantansa game da ainiyin abin da ke damun shugaban.
'Yunkurin kisa'
Buhari mutum ne mai farin jini a wajen talakawa a yankin arewacin kasar.
An yi zaton zaman Buhari tsohon janar na soja, kana sanin halinsa na bin doka da oda zai ba kasar damar fuskantar kalubalen ta'adancin masu kaifin kishin Islama da suka mamaye yankin arewa maso gabashin kasar.
Shi dai Musulmi ne daga Daura a jihar Katsina, kuma tuni ya bayar da goyon bayansa ga tsarin aiwatar da shari'a a arewa, wanda ya sanya a baya dole ya fito yana kare kansa daga zargin da ake masa na cewa shi mai tsatsaurin ra'ayin addini ne.
Fiye da mutum miliyan uku ne rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a arewa maso gabashin kasar
Hakan ya yi masa illa a lokacin zaben shekarar 2003 - lokacin da ya kasa samun goyon bayan Kiristoci da ke kudancin kasar.
Na san masu yi min fatan mutuwa — Buhari
Aisha Buhari na taya mijinta kamfe
Kungiyar Izala ta bukaci mabiyanta su zabi Buhari a 2019
Amma bayan da ya tsallake rijiya da baya a lokacin da aka kai hari kan jerin motocin da ke masa rakiya a Kaduna, harin da ya yi kama da irin wanda kungiyar Boko Haram take kai wa na kisan wadanda ke adawa da ita, Buhari ya yi alkawarin kawo karshen ta'addanci cikin watanni idan aka zabe shi.
Sai dai har yanzu rikicin Boko Haram yana ci gaba da zama kalubale a kasar, musamman a 'yan watannin nan.
Shugaba Buhari ya taba alakanta rashin karfin halin shugaba Jonathan a dalilin da ya jawo tabarbarewar al'amarin, da kuma kin yarda da kiraye-kirayen da ake masa na ya hau teburin tattaunawa da kungiyar.
Har yanzu ana tuna shi da matakan da ya dauka a lokacin yana kwamandan sojin Najeriya a shekarar 1983 - lokacin da wasu sojiojin Chadi suka kwace wasu tsibirai mallakin Najeriya - a yankin arewa-maso-gabas, yankin da sojojin kasar ke rike da shi bayan da ya fatattaki masu harin.
"Yaki Da Rashin Da'a"
Ya mulki Najeriya daga watan Janairu na 1984 har zuwa watan Agusta na 1985, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Disamba na 1983.
Wannan lokaci ne da ake tunawa da shi don tsananin aiwatar da yaki da rashin da'a da kuma take hakkin dan Adam da gwamnatinsa ta yi.
Shin Buhari na samun nasara a yaki da cin hanci?
Matar da ta 'damfari' mutane a fadar Shugaba Buhari
Bayani kan Shugaba Muhammadu Buhari a takaice:
Shekararsa 76
An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
An hambare shi a juyin mulki
An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
Mai ladabtarwa ne - a kan sa ma'aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka makara zuwa aiki
Musulmi ne daga arewacin Najeriya
Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa
Akwai bambamcin ra'ayi game da tasirin mulkin sojin Buhari na watanni 20 da ya yi.
Kimanin 'yan siyasa 500 da ma'aikata da 'yan kasuwa ne aka tsare a kurkuku a lokacin wannan yaki na almubazzaranci da cin hanci da rashawa.
Wasu mutane suna ganin hakan a matsayin yin amfani da karfin soji da ya wuce misali.
Wasu ko suna tuna wannan lokacin a matsayin wani yunkurin yaki da cin hanci da yaki ci yaki cinyewa, abin da ya dakile ci gaban Najeriya.
A dalilin wannan ne 'yan siyasa har ma da sojoji da farar hula suka shaide shi da halin gaskiya da rikon amana.
Buhari ya damu da kashe sojojin Najeriya a Borno
Na fi Buhari yaki da cin hanci da rashawa — Jonathan
Daya daga cikin abubuwan da ya yi shi ne bai wa 'yan Najeriya umarnin bin layuka a tasoshin shiga mota kana ya tura sojoji masu rike da bulala su sa ido.
An dinga ladabtar da ma'aikatan gwamnatin da aka kama su da zuwa wurin aiki a makare ta hanyar sanya su yin tsallen kwado.
A shekarar 2015 jam'iyyun adawa sun hada kai don ganin an kayar da PDP a zaben shugaban kasa.
Ya kuma gabatar da wata doka mai tsauri ta sanyawa 'yancin 'yan jarida takunkumi, inda har aka daure wasu 'yan jarida biyu a lokacin mulkin sojansa.
A hannu guda kuma, kokarinsa na farfado da tattalin arziki inda ya dakatar da shigo da kayayyaki daga kasashen waje ya jawo mutane da dama sun rasa ayyukan yi tare da durkushewar kasuwancinsu.
Farashin kayayyaki sun tashi inda rayuwa ta sauya, wanda hakan ya sanya Janar Ibrahim Babangida ya yi masa juyin mulki ranar 27 ga watan Agustan 1985. An daure Buhari a kurkuku na tsawon wata 40.
Janar Babangida ya so ya yi gaggawar bai wa farar hula mulki, wanda Janar Buhari bai dauki hakan da muhimmanci ba.
'Mutane ya rage naku'
Janar Buhari ya ci gaba da kare dalilin da ya sa ya yi juyin mulki a ranar 31 ga watan Disambar 1983.
A watan Oktobar 2005 ne Janar Buhari ya ce, "Ya rage wa mutane. Idan kuna son shugabanci na gari, to ba bu bukatar mulkin soja.
"An samu mulkin soja ne a lokacin da ya zama dole ana bukatar hakan, kuma wadanda aka zaba na farar hular ba su yi abin a zo a gani ba."
A lokacin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ke shugabanci na mulkin soja a shekarar 1970, Buhari ne ke rike da muhimmin mukamin ministan man fetur.
Buhari ya ce da gangan APC ta tauye hakkin masu son yin takara
Buhari ya amince a kara wa 'yan sanda albashi
Amma dangantakarsu ta yi tsami bayan da Buhari ya hambare gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari, wanda shi ne ya ci zaben da Mista Obasanjo ya shirya.
Wannan ya ci gaba da jawo kace-nace game da matsayar Buhari dangane da demokuradiyya.
Obasanjo yana cikin mutanen da suka goya wa Buhari baya a zaben 2015, amma daga bisani tsohon shugaban ya soki manufofin Buhari kuma ma har ya ce ba ya goyon bayan tazarcensa a 2019.
Kafin shekarar 2015, Obasanjo wanda ya ci zaben shugaban kasa har sau biyu a karkashin inuwar jam'iyyar PDP daga 1999 ya ce:
"Buhari ba zai zama kwararren mai inganta tattalin arziki ba, amma zai zama shugaba mai karfin zuciya wanda ba za a iya tankwara shi ba, zai kuma kasance shugaba mara wasa da aiki."

Hausa music ::: Tasi'u Tk. So

Music :::  Tasi’u T.k started the year with a bang!! This smooth Afro-Pop song is a must listen. Accompanied with amazing
visuals that snatches the mind of its Audience, this song will definitely capture your heart. This is the revolution we need in the Nigerian Music Industry. Young minds who bring Nigerian Music to life. Welcome to the Era of Vibes, this Nigerian Born Kaduna Artist “Tasi’u T.k” is one to watch out for.
So is a soothing mid tempo Afro-Pop song with an addictive percussive rhythm that is sure to have you grooving. Produced by PCB, Tasi’u T.k vocal and lyrical delivery certifies this track as one for your speakers.
Watch & Download Tasi’u T.k – So Below:-
             DOWNLOAD VIDEO HERE

Naija music ::: VanceCarter – Dance (Prod. by Yubskie) Ft. BR

Music .:: New School Rapper/Singer ‘VanceCarter” features Overall finest acr ” BR ” on his first single of the Year titled ” DANCE ” Produced by Youngest Producer “YUBSKIE” from the title of the song You know its gonna be groovy, so download and enjoy.             DOWNLOAD MUSIC HERE

Naija music ::: Lil Touch – Combine

Music :::: Lil Touch,a student of Olabisi Onabanjo University comes through with a fresh new joint tittled Combine. This outstanding tune is definitely a tune you need to add to your playlist. Produced by Sensational Hit Maker,Mystylez.
Listen & Download “Lil Touch – Combine” below:-

              DOWNLOAD MUSIC HERE

Labaran chikin kasa Nigeria :: me duniya ina zaki damu ?

An tsinci wani jinjiri kunshe cikin tsinma a daji a kauyen Giri da ke Gwagwalada a Abuja
- Wasu matasa ne da ke hanyarsu ta zuwa gona suka ji kukan jinjiri kuma suka bincika suka gano shi a cikin daji
- Sun koma kauyen sun sanar da mutane kuma daga bisani aka kai jinjirin gidan marayu na Gwagwalada
An tsinci jinjira da wata mata ta jefar a daji
An tsinci wani jinjiri da wata mata da ba san ko wacece ba ta jefar da shi a cikin daji a kauyen Giri da ke unguwar Gwagwalada na babban birnin tarayya, Abuja.
Daily Trust ta ruwaito cewa wata mata a kauyen na Giri mai suna Ramatu Danjuma ta ce wasu matasa ne da ke hanyarsu ta zuwa gona suka gano jinjirin kunshe cikin zani a safiyar ranar Talata.
Ta ce kukan jinjirin ne ye janyo hankulan matasan hakan yasa suka nemo inda ya ke sannan suka dawo kauyen suka sanar da mutane abinda suka gano.
DUBA WANNAN: Legas: An kama manyan 'yan kasuwa dake daukar nauyin 'yan bindigar Zamfara
" Ina tsamanin mahaifiyarsa ta jefar da jinjirin cikin dare ne. Wasu matasa da ke hanyarsu ta zuwa gona ne suka ji kukan jinjiri kuma bayan sun gano inda ya ke a cikin dajin suka dawo kauyen suka sanar da mutane," inji ta.
City News ta gano cewa daga bisani wata dattijuwa a kauyen da dauki jinjirin ta kai shi gidan marayu da ke Gwagwalada.
Anyi yunkurin tuntubar Kakakin 'yan sandan babban birnin tarayya, DSP Anjuguri Manzah domin ji ta bakinsa amma bai amsa wayarsa ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aike masa ba.